Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Namra ta cige baki, gaba daya yau Hurriya ta yi ruining din day dinta, daman jiya ta gama sanin Salim ba ita yake so ba, yau kuma ta hada mahaifiyarta da Hajiya, ga kuma Captain da ta saka ya zage ta kuma ya zargeta da abun da bata san kuskure a cikin aikata shi ba.
“Wai yaushe ma ya dawo?”
Namra ta sake tambaya.
“Ni kaina ban sani ba shekaranjiya ma na yi waya da Hajiya Turai amman bata fada min Captain zai zo, amman dai da alama yau ya shigo garin nan, duk dai zuwan nasa ba sani ake ba”
“To yanzu ya zaki ce masa?”
“Cewa zan yi na yi magana da mahaifinta yace be yarda ta dawo ba, ban da ma daukarwa rai ya cusa kansa a wannan rigimar”
“Kika san abun da ta fada masa”
“To ina ta san shi ma yaushe rabonsa da gidan nan”
“Zata iya ganeshi ai, kin san ya taba marinta, tawun motarsa ma da aka fasa kika ce Hajiya ce ba Hajiya bace ita ta zuga Hamad ya zo ya fasa masa tawun mota”
Momy ta watsa mata wani kallo
“Ke tsaya… Kina nufin tayun da aka taba fashewa na Captain Hamad ne?”
“Wallahi shi ne”
“Oh yara dai sun zame mana masifa”
Namra ta tabe baki tare da duba wayarta sannan ta tashi tsaye ta nufi stairs, kamar wanda ta yi mantuwa sai ta dawo ta nufi kofa.
“Ina zaki je?”
“Sakon Hajiya Binta zan isarwa Hajiya”
“Dawo kyaleta idan ta matsu ta fada mata da kanta ai tana da wayarta ta kira wayarta ta fada mata mana”
“Momy kara na isar mata ai, kar ni ma na yi laifin gurin Hajiya kin san bata hada Hurriya da kowa ba a gidan a nan”
Momy ta dauke kai ba tare da tace komai ba, wanda ke nuna alamar ta aminta Namra ta tafi kenan sai dai ba dan ranta ya zo haka ba. Namra ya fice tana juya yawarta a hannun har lokacin sake saken yadda Hurriya ta shirya komai take, me ta fadawa Captain kuma me ya sa ran Salim ya bace shi ya fi tsaya mata a rai, har ta yi kamar ta kira shi sai kuma ta fasa ganin shi ma kamar baya son ta sani, kuma ita Yaya ce be kamata ta shige masa ba. Sai da ta kalli Khairy dake ta fito falon sannan ta dauke kai ta shiga, daman ita da Khairy yanzu babu mai yi na wani magana tun a lokacin da sa’insa ta shiga tsakaninsu saboda iyayensu. Sai da Namra ta shige sannan Khairy ta dauke idonta daga kofar falon Hajiya ta nufi gate, tana ficewa a karamin gate ta nufi babban masu gadin suka bude mata ta fita. Tafiya mai nisa ta yi sannan ta isa gaban wata mota, sai da ta fara kwankwasawa ya sauke gilashin sannan ta bude ta shiga baya ta zauna.
“Yarinyar nan fa bata nan amman baka yarda ba”
“Ba zaki iya fitowa da ita ba shi ne kawai”
“Wallahi bata nan, Appamu ya koreta ta koma gidan Kakarmu da zama”
Ya juyo ya kalleta.
“Saboda me?”
“Mumafurci ta yi shi kuma da ya ji ya koreta”
“Munafurcin me ye?”
“Ba abu ne da ya shafe ka ba, magana ce ta cikin gida, ni dai yanzu mu kare abun da zamu yi ina son na koma kar Yayana ya dawo ya nemi ni bana cikin gida”
Ya daga kafadunsa.
“Kin san abun da ya kawo ni ai”
“Ni ba zan iya maka magani ba Adam, kullum kana damuna da maganar yarinyar nan, ni fa ina da damuwa baka san abun da yake damuna ba”
“Duk wata damuwa taki mai sauki ce saboda na san ba zata wuce ta kudi ba, amman ni kin san kudi ba za su magance matsala ta da yarinyar nan ba saboda kin bata komai”
Cikin matukar damuwa da gundira da dora mata laifi da yake ta ce.
“Yanzu me kake so na yi? Ni ban bata ka ba Adam, kuma ba a saka soyayya da karfi ai da ka sakawa kanka ko?”
“So nake ki gyara, ki gyara duk wani abu da na bata yarinyar nan ta dawo tana kula ni”
“Ban san yadda zan yi haka ba Adam, kuma kai kanka ka san ba auren yarinyar zaka yi ba, ita kuma tana da wahalar sha’ani ba irin mu ba ce”
“Ta ina kika karanta cewar ba aurenta zan yi ba? Ina aka rubuta hakan a goshina? Kin gani ko ke kika kara bata abubuwa”
“Kai baka san yadda zaka yi ta so ka ba ne Adam, kai ba namiji ba ne, ka dame ni da zancen yarinyar kamar ita kadai ce mace a garin nan”
“Ba ita kadai ba ce, amman ita nake so yanzu kuma kin san yadda zuciya ke hana mutum zaman lafiya idan be bata abun da take so ba”
“Adam akwai matan da suka fi Hurriya kyau a duniyar nan, kuma babu wanda zaka ce kana so bata amsa maka ba, ita Hurriyar nan fa makauniya ce, bata gani sai da gilashi”
“Ko gurguwa ce haka nake sonta…”
Ya mika hannunsa a front seat daga kasa ya dauko wata ledar ta mika mata.
“Kudi ba matsala ba ce, zan iya biyanki ko nawa ni dai ina son ki ja hankalin yarinyar ya dawo gareni, kin san yadda nake daga hankali idan ina son abu”
Ta mika hannu ta karba ta bude kudi da ba zata iya fadar adadinsu a yanzu, kudi ne mai yawan gaske kuma bata yi mamaki ba, daman cikin familynsu ya fi kowa wasa da kudi, wannan ya saka yan mata da yawa suke lake masa. Ta daga kai ta kalleshi
“Adam.. Me Hurriya take da shi da ya fi na sauran matan duniyar nan?”
“Tana da kyau, tana da jiki da sifar da nake so a jikin mace, kuma babu ruwanta da magana ina son mace haka, and zan iya nuna ta a ko’ina as my girlfriend kowa ya gani ya san ya zabo mai kyau”
“Ba zan iya sakawa Hurriya ta so ka ba Adam, ko da kuwa duniyar nan da abun da yake cikinta ka mallaka min, ba zan iya cusa soyayyarka a zuciyarta ba saboda tana da wahalar sha’ani kuma tana da tsoro, kuma ta riga ta san waye kai, ko dan gudun gargadin da Appa yayi nata da kuma Yaya Yasir dole ta guje maka”
Ya jinginar da kansa yana busar da numfashi.
“But zan iya maka taimakonka ta wata hanyar idan hakan zai wadatarta kuma idan hakan zai saka ka daina dora min laifi”
Ya juyo ya kalleta.
“Wane irin taimako? Ni bana da burin da ya wuce yarinyar nan ta so, abun da kika kasa fahimta shi ne yarinyar tana da karfin jini jan hankalin mutum, kuma idan ta shiga zuciyarsa tana da wuyar mantawa abun daga jini ne, baki san iya yadda na yi kokarin cire yarinyar a zuciyata ba amman sai kara shiga take har mafarkinta nake Khairy”
“Ba zaka ki wannan shawarar tawa ba, amman ba yanzu za mu yi maganar ba sai idan na shiga gida sai mu yi waya”
“Zamu iya maganar a yanzu ai, zai fi saboda gani ga ki”
“Yayana zai iya dawowa ya nemi ne, idan kuma ya gano ina nan zamu shiga matsala daga ni har kai”
“Ki fada min a nan zai fi”
“Matsala ta da kai kenan Adam, ba ka daukar shawara kuma baka yi ma mutum izuri, kanka kawai ka sani ni ina kokarin ganin na cireka a matsala kai kuma kana son jefani, ba abu ne na tashin hankalin ba na ce ka bari na tafi gida idan na natsu sai mu yi magana kamin lokaci ma wata kila na kara samun mafita”
Ba dan ransa ya so ba ya sauke ajiyar zuciya ya daga mata kai.
“Shikenan, amman zan fada miki gaskiya idan kika ci wannan kudin ban samu abun da nake so ba”
Ya tsaya tare da busar da iskar bakinsa.
“Ba zan duba abotar mu ba, kuma kar yi mamakim duk abin da zan miki”
“Hakan ma ba zata faru ba”
“Okay”
Ta bude motar ta fita sannan ta miko hannu ta dauki kudin, be bar gurin ba sai da ta shige cikin gida. Sai da Khairy ta nemi guri ta boye kudin a Garden saboda tana tsoron Hajiya ko Yayanta ya ganta da kudi mai yawa haka a leda, tsayawa ta yi ta natsu sannan ta dawo ta nufi kofar falon.
Ruma na zaune tana kallon Hajiya Kaltume dake ta zuba ruwan bala’i na sakon da Namra ta isar na Hajiya Binta, ji take kamar ace mahaifiyar mijin nata tana kusa da ita ta amsa mata daidai da abun da ta aiko aka fada mata.