VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Momy wannan nake so, Hurriya ta dauki bakar”

Momy ta tsaya kallonta.

“Idan ta dauka ke zaki biya? Ka ji min wani rainin hankali”

“Momy toh ai na ga na shagonki ne”

“Idan na shago ne mutuwa na yi balle ki ci gado har ki dauka riga mai tsada ki ce abawa Hurriyya?”

Namra ta juya ta kalli Hurriya sannan ta juyo ta kalli Momy tana mana alama da zata iya ji.

“Ta ji mana, tsoronta nake? Ke ce baki san ciwon kanki ba har kika hada kanki da ita, kina kallo a gidan nan duk kudin da mahaifinsu zai bada na siyen abu sai na ciya na siyo muku wanda ya fi na sauran yan’uwa, amman yanzu har kika maganar ki saka riga Hurriya ta saka irinta”

Da kamar mamaki Namra ta ce.

“Ubanmu daya da ita fa, kudin da Appa zai bata su zai ba ni duk daya ne”

“Eh amman ai ina kara miki? Tufafin da kuke sakawa wake sska su a gidan nan? Karki sake min wani abu makamancin wannan, rai na a bace yake kin kara min wani”

“Me ya faru Momy”

“Kaltume ce wai kidnappers sun kamata suna neman milyan dari”

Momy ta fada tana kiran sunanta domin ita kadaice a gidan bata sakawa Hajiya Kaltume ta ce Hajiya sai dai ta ce Kaltume kawai. Hurriya ta juyo da sauri jin abun da Momy take fada, Namra kuma ta zaro ido.

“Innalillahi daman sai da na fada tana ina yanzu?”

“Ke kin yarda? Ai talaka babu abub da ba zai iya ba, wannan Kaltume zata iya kidnapping din kanta da ta karbi wannan kudin gurin Alhaji, balle tana ganin yadda nake tafiyar da kasuwanci ai abun yana tsone mata ido”

“Haba Momy taya? Kuma har wannan kwanakin bata fito ba?”

“Ke makira ce wannna matar fa, ni na san yadda na zauna da ita, kin ji ta a waya sai kukan munafurci take wai wani idan ta kara sati a gurin mutuwa zata yi, tana cikin bala’i da masifa a Alhaji ya taimaka ya kawo kudin da wuri hmmm”

Momy har wani kwaikwayon muryarta take tana nufar hanyar Kitchen Namra ta rufa mata baya dan kara jin labari, ita sam bata yarda an sace Hajiya Kaltume ba ta fi yardar Hajiya Kaltume ce ta sace kanta. Hurriya mamakin ya hana ta cigaba da cin abinci mamakin jin cewar an sace Hajiya Kaltume take, da dayan bangaren kuma tana mamakin yadda Momy take ganin kamar ita da Namra suna da banbanci bayan uba daya ya haife su, tana mamakin yadda Momy take duban Hajiya Kaltume ma dake da tarin rufe asiri a gidan tana ganinta talaka. Da sauri Hurriya ta cire hannunta a abinci ta fice daga falon zuwa bangaren su Khairi.
☆❁ ❁☆

Hello Habibaties
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

9️⃣

Hurriya na shiga falon Hajiya Kaltume ta fara rabon ido ganin yadda kowa yayi jigun, wasu daga yayanta kuma suna amsa waya suna kuka. Gurin da ta tafi wayo ta nufa wato gurin yayanta ta tsaya kusa da shi tana kallonsa har ya gama wayar sannan ta ce.

“Yaya wai garkuwa aka yi da Hajiya?”

Kamin ya bata amsa Khairi ta watsa mata harara.

“Tsohuwar munafuka, hala dadi kika ji?”

“Dadi dai? Me ye abun jindadi a ciki da har zata ji dadin? Wace irin magana ce wannan?”

“Toh Yaya idan ba haka ba, me yasa take tambaya?”

“Bata da hakkin sani ne? Ni kuna bani mamaki a gidan nan Wallahi, miye laifi a ciki idan ta tambaya? Karki bata min rai yanzu na fara dukanki”

Yasir ya karashe maganar yana nunata da yatsa, sai ta dauke kai domin ta sani sarai zai iya, ba wani jutuwa suke da juna ba. Ya dubi Hurriya dake gefensa tsaye.

“Eh sace ta aka yi, mu ma yanzu Appa ya zo mana da maganar sun ce za a ba su miliyan dari”

A take hankalinta ya tashi, tana son ta sake cewa wani abu tana tsoron kar Khairi ko Salma su kwatseta, dan haka ta ja bakinta ta yi shiru tana cigaba da sauran yadda ake ta kiran yan’uwa ana fada musu.

****       ****         ****

A haka sai da Hajiya ta kara sati daya a hannun mutanen nan ita da Hajiya Fatee domin police aka saka a lamarin su kuma suka hana a aika da kudin, suka ce za a gano inda take, sai da Appa ya ga abun na su ba mai yi ba, ga hankalin yaransa da yan’uwan Hajiya Kaltume ya tashi ya nemi sassauci suka rage kadan ga miliyan dari, a sake neman sauki, daker da addu’a da sudin goshi aka samu suka sauko a miliyan goma, bangare Hajiya Fatee ma haka suka karba, Appa ya hada kudinaka rasa wanda zai kai, sai da wani kanen Hajiya Kaltume yayi jihadi yace shi zai tafi kai musu kudin, ranar da zai tafi suka fadi inda zai tsaya a dajin su zo su tafi da shi, haka kuwa aka yi Fadeel ya kawo nasa kudin aka hada da na Appa suka shiga mota aka kaishi har inda suka bukata suka fito suna masa addu’a, su kawo wajen gari suka tsaya. Ba zan wani jima ba suka kira suka ce aje a dauke ta a wata gona dake nan dogon dutse a nan za su aje su. Abun ka da mai nema Yasir da Fadeel da Uncle din Fadeel din suka nufi gurin da moto suna gudu kamar ba za su je su same su a gurin ba. Kamin su isa kowannensu hankalinsa ya tashi kuma zuciyarsa ta cika da zullumi, domin suna tsoron kar su je su tararda gawarta domin sun saba haka wani lokacin sai su ce aje a dauka sai an tafi a tararda mutum a mace.
A bakin titi suka faka motar suka fita suka shiga cikin gonar domin dubawa, Yasir da waya a kunne yana fadawa Appa sun isa gurin Appa kuwa sai gargadi yake masa.

“Yasir ku kula da kyau, zai iya yiyuwa dabara suka muku saboda idan kun shiga gurin su sace ku”

“Aka yi mana Addu’a Appa In Shaa Allah babu abun da zai faru, fatanmu dai a samu Hajiya da rai”

Yana rufe baki ya ji muryar Fadeel yana fadin ya karaso nan gasu a nan, da sauri Yasir ya katse wayar ya nufi gurin, Hajiya Fatee ce da Hajiya Kaltume daure jikin itace, kansu babu ko dankwali sai wani zane atamfa kala daya da suka yafa kamar wasu yan kauye sun yi yaushi kai kace allayahun da yayi sati ne a daure, fuska ta yi burun-burun kana ganin kasan an dade ba a sadu da ruwa ba, baki ya bushe idanuwa sun kode kamar wadanda suka kusa kusantar rame. Hajiya na ganin Yasir ta fashe da kuka, Hajiya Fatee kuma ta fara zubar da hawaye.

“Alhamdulillah Alhamdulillah”

Shi ne abun da sukr ta fada bayan sun kwance su.

“Ku yi sauri muje kar su biyo sawunmu, Sannu Hajiya”

Fadeel ya fada yana kallon mahaifiyarsa cike da tausayawa.

“Bana iya tafiya Fadeel bana iya komai”

Tana maganar tana nishi hawaye na mata zuba, Hajiya Kaltume kam kuka take riri domin da yanzu da aka sako su da kuma lokacin da aka kama su duk yayi mata kamar mafarki, ita kadai ta an bakar azabar da suka sha. Duk yadda Yasir ya so su yi sauri hakan be samu ba saboda Hajiyoyin duk basa iya sauri tafiyar ma sai daker gashi jikin ba kadan ba balle yayansu su ce za su taimaka musu, a haka dai suka isa gurin motar, Hajiya Fatee ita ce mai tafiya kamar mai tatata, Hajiya Kaltume ce mai dan kuzari shi ma ba wani da yawa ba sai na karfin hali. Hankalin kowa be kwanta ba sai da suka isa gida, domin kin amincewa suka yi da maganar Appa da kuma na yaransu cewar a tafi da su asibiti a duba lafiyarsu, Hajiya fatee ce ta fara nuna karfiya sannan Hajiya Kaltume ta rufa mata baya. Daga gidansu Yasir Fadeel ya dauki mahaifiyarsa ya fice da ita zuwa family house dinsu bayan ta yi wanka, sai dai ta kasa saka komai a baki duk kuwa da irin lallabata da Fadeel yake. Be isa gida ba Yasir ya kira wayarsa yana fada masa wai sun kira sun ce shi ma wanda aka aika yana da mai da alama za a samu wani abu dan haka sun rike shi sai an bada miliyan 20.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected