Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Appa ina kwana”
“Lafiya kalau Hurriya an tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Ta mika hannu biyu zata karba, Yasir ya rigata ya karbe yana dariya kamar yadda ya saba, kasancewar bata a cikin yanayin farinciki sai kawai ta yi murmushi ta hade hannayenta. Appa ya dauko wani ya mika mata.
“Karbi, ina Hamad?”
Ta saka hannu biyu ta karba taba ba shi amsa.
“Yana bus ya ce shi ba zai karba ba yau”
Appa ya ji babu dadi sai dai be nuna ba kuma be sake cewa komai ba, Hurriya har ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Appa.
“Appa yaushe Amma zata dawo?”
Kallonta kawai mahaifinta yake, kamar yace me yasa kika min wannan tambayar domin be gama saka kalar amsar da zai ba su ita da Hamad, musamman ma ita da take da shakuwa da shi sosai wata kila Hamad zai bar abun a zuciyarsa dai dai yayi ta fushi da shi. Yasir ne yayi hanzarin tarewa Appa numfashin da ya rasa ina sauke shi.
“Hurriyya idan zaki yi magana mai tsada da Appa, daga ke sai shi ya kamata ku yi, ki daina yi a gaban mutane kin ji”
Ta amsa masa da kai, sannan ta kalli Appa
“Na gode Appa Allah ya saka da alheri”
Ta juya ta fara tafiya zuciyarta babu dadi. Godiya ce ta yi masa irin wadda ta saba masa a duk lokacin da ya bata chocolate din ko kuma yayi mata kyauta kasancewar abun da Amma ta koya musu kenan, amman a yau sai ya ji godiyarta a wata sigar ta dabam, yake jin kamar abun da ya aikatawa mahaifiyarsu ne take masa godiya a kai, gashi dan murmushi da far’a da kuzarin da yake gani a fuskar yarsa yau ya kau, dan’uwanta kuma ko ganinsa be yi ba.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Shi ne abun da ya iya furtawa yana binta da kallo zuciyarsa na masa zafi, tunanin dama da hadu na kokarin hade masa su rikita masa kwakwalwa. Yasir ya kalleshi sai dai be ce komai ba.
“Idan sun dawo makaranta kai ko daya daga cikin direbobin gidan nan wani ya kai su gida su duba Amma”
“Toh Appa In Shaa Allah”
Appa ya juya ya koma ciki, Yasir na binsa da kallo kansa a daure yana mamaki wane kalar laifi Amma ta yi masa da har ya yanke wannan tsatsauran hukunci haka.
*** *** ***
Ruma ta turo kofar dakin ta tsaya daga jikin kofar ta kalli Khairi dake zaune gaban madubi tana shafawa bakinta magani ta ce
“Khairi wai Ina Hajiya tace miki zata tafi?”
“Ba ni ta fadawa ba, Maama ta ce gidan Hajiya Fatee zata tafi”
“Toh amman har yanzu zata dawo ba? Na kira wayarta be shiga”
“Maybe can zata wuni, ai dole dai idan dare yayi kin san zata dawo”
“Khairi karfe 6:30pm ake magana fa, kuma ta fita tun safe”
“Aa Ruma kin cika matsala, Hajiya ai ba yarinyar ba ce idan lokacin dawowa yayi ai ita zata dawo, kika san abun da ya saka ta dade? Kin san dai Hajiya Fatee aminiyar Hajiyarmu ce, waya san me taje yi a gidan”
Khairi ta amsa mata da kamar fada domin ta hana ta shafa maganin da take cikin salama sai damunta take da tambayoyi. Ruma ta tabe baki ta fito taja mata kofar tana sake gwada line Hajiya domin ita idan Hajiya bata a gidan duk jinsa take ya zama dabam wannan ya saka wani lokacin ma har bin Hajiya take idan zata fita, kusan duk kawayen Hajiya sun san yar autar Hajiya Ruma saboda yawan lake mata da take. Har ta isa dakinta gwada line take amman kiran yaki shiga baturiyar sai tabbatar mata take da ba a samun Hajiya.
☆❁ ❁☆
8️⃣
Suna shigowa cikin gidan Gwaggo Hurriya ta shiga dakin da sauri tana neman Amma. Gwaggo ta yi dariya tana daurawa jikarta dankwali
“Maraba da Hurriya yanzu ake tafe”
“Eh Gwaggo ina wuni”
“Lafiya kalau ina Hamad?”
“Shiga nan shigowa, Gwaggo Ina Amma?”
“Tana dayan dakin dake kusa da na su Rukayya”
Da sauri Hurriya ta tashi ta fice daga dakin Kakarta zuwa dakin da Amma take, tana shiga dakin ta fada jikin Amma kamar bata san tana dauke da cikin kanensu ba, sai kuka ya biyo baya ta kankame Amma sosai kamar za a kwace nata ita. Cikin karfe hali da dauriya irin na uwar da bata son raunin yayanta ya kamata har ta yi kuka a gabansu ta shafa bayan Hurriya tana dariyar da sautinta yaki fitowa, hakan kuma ba karamin taimakawa idonta yayi ba gurin zubar da ruwan hawayen da a da su kwana a idonta. Kanwarta Rukayya ta bata fuska sosai kamar ta fasa kuka.
“Amma da baki nan gidan babu dadi, kuma Appa ya kwashe kayanki daga gidan”
“Na sani, ya aiko min da su nan ai, suna nan a zuba a gareji, wasu an saka a falon waje”
Hurriya ta dago tana kuka ta kalli Amma.
“Ba zaki dawo ba kenan? Khairi ta fada min Appa ya rabu dake?”
“Na fada miki tun ranar ai, abincina ya kare a gidanku, ina Hamad”
Amma na rufe baki Hamad ya karaso gurin kofar sai ya tsaya yana kallonsu kamar wani bako.
“Hamad shigo mana ya ka tsaya a jikin kofa”
Rukayya ta fada, sai ya nufo cikin dakin yana jin wani irin tausayin mahaifiyarsa da ya kasa nunawa a fuskarsa, sai dai sanin halinsa da Amma ta yi ya saka ta fahimci akwai damuwa a tare da danta domin fuskarta babu walwala kuma ba hade rai yayi ba alamar fushi, yana a wani yanayi ne da ita kadai take gane damuwarsa.
“Hamad kuna nan kuna ta fadan ko?”
“Ba mu yi fada ba, ba mu yi fada ba Amma, amman dai gidan babu dadi…”
Dorawa ta yi da labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan ciki har da komawarsu bangaren Momy da suka yi.
“Daman gidan ko da ina ciki ya kuke zaune balle bana nan, sai dai ku yi ta hakuri karku saka komai ranku”
“Ni dai na ce Bappanku ya tafi gurinsa yayi magana da shi, yaran nan ya bar su zauna a gidan nan idan ba haka ba, wannan matan uban na su za su iya saka musu guba su mutu ma”
Cewar Gwaggo a lokacin da take kokarin shigowa dakin. Sai Amma ta amsa mata tana hawaye.
“Allah ya fi su Gwaggo, na san Allah baya bachi kuma baya son zalinci, zai kare su, amman abu ne mai wahala Alhaji ya yarda yaran nan su zauna a gidan nan”
“Amma me yasa Appa ya sake ki?”
Hamad ya tambaya kai tsaye yana tsare ta da ido.
“Ban sani ba Hamad, Wallahi ban sani ba, da ace na san laifin da na yi masa wata kila da zan fi jin sanyi fiye da yadda nake ji a yanzu, shi kan shi ya ce ban masa laifin komai ba”
“Saboda Hajiya ne? Ko Kuma Momy”
Amma ta kama hannunsa ta rike
“Ba saboda kowa ba ne, kar kaje ka yi ta fada da mutane wahala zaka sha a gidan nan, dan Allah ka zauna lafiya da kowa Hamad wannan fushin da saurin kai hannu ka daina, ku kenan Allah ya ba ni sai wannan idan na haifa, ban sani ba ko zan kara wani ko kuma iyaka kenan, dan Allah ku hada kanku ku zauna lafiya, ina gidan nan amman tunanina yana can tare da ku saboda na san yadda kuke yawan samu tsabani da juna, ba ku mai raba ku a yanzu idan kuka yi fada ma dadi za su ji”
“Be ci abinci Amma tun da kika bar gidan nan, da safe ma tea kawai ya sha”
Amma ta dauke idonta daga barin kallon Hurriya dake fada mata ta kalli Hamad.
“Saboda me? So kake ka jawa kanka wani ciwo kuma?”
Kamar an zunguro idonsa haka ya fara hawaye yana kallon mahaifiyarsa, duk yadda ta so ta daure sai ta kasa ita sai da kukan ya ci karfinta balle Hurriya da ke da raunin zuciya. Rukaiyah ta share hawayenta.
“Kai Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un, Wallahi idan raba ku aka yi an ci amanarki an ci amanar yaran nan, mu ma kuma anci amanarmu an daga mana hankali”
Gwaggo ta girgiza kai cike da tausayawa.
“Toh Allah ya kyauta, arzikinsu ma suna da wayo da ace kanane ai da sai sun fi shan wahala, kuma ubansu yana sonsu za su samu sauki ta wani bangaren”