VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Wato ta koma can zata fara hada mu da Hajiya ko? Ita dai Iyami ta kawo mana bala’i kawai a cikin gidan nan ta hana mu zama lafiya, na kashe maciji amman ban tare kai ba shi ne a nan, yar guda guda ta zame mana fitina a gida”

Ruma ta kalli Hajiya Kaltume cikin yanayin bakinciki har idonta na cika da kwalla ta ce.

“Haba Hajiya yanzu kuma me ye laifin Hurriya a nan, fadan da Hajiya Binta take yi saboda abun da kuke mata ne, kuma gaskiya ta fada, da ni ce ko Khairy ba zako bari wani na tafi ba, ita ma Momy da Namra ce ba zata bari ta tafi ba, amman kalli yadda Appa ya koreta kamar wata bare, Hajiya komai sai kin dorawa Amma laifi matar nan bata lafiya magana ma wannan bata iya, shin ya kuke son Hurriya ta yi? Ta rasa dan’uwa mahaifiyarta babu lafiya yanzu kuma Appa ya koreta kuma still ita kike dorawa laifi”

Hajiya Kaltume dake jin kamar ya janyo Ruma ta rufe da duka ta shiga fada a tsawa.

“Da uwarta bata zo ta aurar min miji ba duk zamu san da wannan matsalar ne? Da yanzu za a haifi Hurriya har ta fara hada munafurci ne? Da take kwance bata da lafiya ni na saka mata ne? Mugun bakin kwadayinta ne ya ja mata”

“Momy ma Appa take aure, amman baki mata masifa kamar yadda kike yi ma Amma, Amma tana son mu tana nuna mana kulawa tsabanin Momy da ko bangarenta bata son mu shiga, kuma idan har suna da laifi to duk laifinsu daya ne domin Appa suka aura”

“Ke yarinya ki iya bakinki, idan baki san gari ba saurari daka, banbancin Iyami da Nafisa ai a bayyane yake, Nafisa a can ya ganta ya auro, Iyami kuma sai da ta gama cin duduniyata ta san sirrin gidana da na mijina sannan ta kulla min gadar zare ta zubar da ni a kasa, ke ba zaki gane abun da ake ji ba, saboda ke yarinya ce baki san me duniya take ciki ba sai nan gaba”

“Ko da hakan ta kasance a gareni, ba zan tsaneta kamar yadda kika tsani Amma da Hurriya ba, da ina ganin kamar ke ce mao gaskiya amman daga lokacin da aka kashe Hamad, sai tunani ya canja wane irin tsana ce zata saka a kashe rai? Idan Amma tana da laifi Hamad fa? Me ya aikata? Yaron nan yana kuka yana kiran sunan Appa da mahaifiyarsa suka fitar da shi, kansa na jini yana ihu yana fadar ayi hakuri yana rike kansa dake jini yana kiran sunan Hurriya daga karshe ma sunana ya koma yana kira, Hajiya na kasa manta wannan duk lokacin da na kalleki wannan abun nake gani, amman ni cewa kika kar a taba ni saboda ina yarki wace irin zuciyata ce wannan?”

Hajiya Kaltume na mikewa tsaye Khairy na turo kofar falon ta shigo da sallama. Hajiya ta yi saurin kallon kofar idonta kamar za su fado saboda razana.

“Wa’alaikussalam”

Ta amsa mata muryarta na yin kamar zata yi rawa. Khairy ta karaso cikin falon tana musu kallon tuhuma domin jiki da fuskar Hajiya Kaltume ya nuna alamar ba lafiya ba, ga Ruma sai kuka take sosai.

“Lafiya?”

“Lafiya Kalau”

Hajiya ta amsa mata da sauri, Ruma ta tashi tana kuka ta nufi stairs, Khairy ta bita da kallo har ta haye sannan ta kalli Hajiya da hantar cikinta ke kadawa ta ce.

“Me ya faru take kuka?”

Abun ka da makiri kuma wanda karya bata yi ma wahala a take Hajiya ta juye abun domin bata son kowa ya ji.

“Munafurcin da Hurriya ta yi ne ya taba ta”

“Munafurci?”

A tsaye Hajiya Kaltume ta zubewa yarta komai da Namra ta fada har ma da wanda bata fada ba, daman ai ba zata bar miya haka nan ba sai ta kara mata gishi da magi.

“Wallahi kawai ki fadawa Appa shi zai yi maganinta idan ba haka ba, shi ma kansa sai ta hada shi da Hajiya, waya sani ma ko ta zugota ta zo tace ba ta yafe masa ba, ko kuma ta rantse sai ya sake ki, daman tana da haushin barin gidan nan da uwarta ta yi, shiyasa ni gaba daya fa bana kaunar yarinyar nan, ga iya jan hankalin maza na bala’i kamar wata rikakkar karuwa”

“Wannan kuma ba banza ba, ai kin san uwarta sai ta wanke ta bata sha, kamar yadda ta sha ta dauke hankalin Alhaji har ya aureta”

“Gaskiya ni ma i doubt wannan farin jini da jan hankalin ba banza ba ne, ba zai yuyi ace kowane namiji farar mace mai kyau yake so ba, to mu ayi yaya da mu bakake?”

Tana fada tana bata rai kamar ta ci magani.

“Ba farin ne kawai ba, har da asiri”

“Daga gani ma ba banza ba, Hajiya tafi ki fadawa Appa ya daukar mata mataki tun wuri”

Ta zauna saman kujera tana ta fushi kamar an mata wani abu, kamin ta shiga Gallary wayarta ta kamo hoton Hurriya ta kura ido tana son tantance abun da Adam ya gani a fuskarta da jikinta da ya nace sai ita, ga Fadeel ma ko a jiya da ya zo sai da ya nemi yin magana da ita.
Hajiya Kaltume da har lokacin a tsaye take ta juya ta nufi kofar dake gefen dinning wanda zata sadata da bangaren Appa, zuciyarta fal da tsoro na maganar Ruma, yanzu ba kisan ne abun da ke ranta ba, fallasar asirinta ne abun da yafi damunta, shekara uku amman Ruma ta kasa mantawa ta saka sakewa gaba daya ta canja tun a lokacin da wannan abun ya faru, idan kuma har zata rika sakin baki haka wata rana dole asirinta zai tonu, ita ta san har ga Allah bata ce a kashe Hamad ba, ba saka an dauke shi dan a kashe shi ba, hasalima ba shi aka je dauka ba, Hurriya ta ce a dauka, tsaitsayi ya biyo ta kan Hamad ashe da rabon ya bar mata baya da kura. Bata san ta isa bangaren Appa ba sai da ta ji ta bugi kofar shiga, a nan ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido ta dafe kanta da hannu daya.

_Kai wayyo Allah… Da na sani ban aikata wannan abun ba, da ma ta asiri na bi kamar yadda na yi ma Iyami, duk gajin hakuri ne ya ja min, yanzu ko yaran nan aka kama suka fadi sunana ai na shiga uku sunana zai bace a duniya, yarana su ji kunya musamman ma matan nan_

A ranta take ta sake sake rashin natsuwa da tashin hankali na kara kusantar ta, ta sauke ajiyar zuciya ya kai sau takwas sannan ta sauke hannunta ta murda kofar ta shiga, babu kowa falon dan haka ta nufi karamin falon Appa da ya fi yawan zama. Yana ganinta yayi saurin sauke wayar da yake ya yanke kiran murmushin dake fuskarsa ya bace.

“Hajiya”

Ta zauna kusa da shi tana fada.

“Na’am Alhaji a nan ake hutawa, Nafisa bata shigo ba?”

“Ina tunanin sai an jima kadan zata shigo”

Yayi saurin rejecting kiran dake shigo masa ya saka wayar silent ya aje ta a gafe.

“Toh bari na yi magana ta kamin ta shigo, wata kila ma ita ce take kiranka kasan sarauniya ce wani lokacin sai dai ta kira ta tambaya abun da kake so ta zo maka da shi, ba kamar mu da bama raina lada ba”

“Aa ba ita take kira ba, wani…. Sakatarenmu ne… ”

Ya amsa kamar marar gaskiya. Cikin rashin kuzari na abun da ya faru ta kora masa da bayanin abun da Hurriya ta yi har Hajiya Binta ta aiko musu da sako. A take Appa ya hade fuska ya bata rai sosai daman a yanzu baya ganin farin Hurriya sai bakinta.

“Wai yarinyar nan me take son zama ne?”

“Toh ka gani dai idan baka daukar mata mataki ba, sai ta lalace kuma nan gaba ba a san me zata yi ba, kai kanka idan baka dauki mataki ba sai ta hada ka da Hajiya, kara tun wuri ka rabata da gidan Hajiya ka maida ita can gurin uwarta ko kuma ka dawo da ita nan din, domin ni dai ina jin tsoron shairin yarinyar nan, kara nan tana karkashin kulawarka zaka saka mata ido”

“Bana bukatar Hurriya a gidana”

Appa ya fada a fusace.

“To ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, in ji kishiyar konanniya, hakuri zaka yi tun da hannunka baya rubewa ka yanke ka yar kar dai ta zauna gurin uwarta ko gidan nan, nan din ma zai fi saboda Hajiya zata iya cewa ba zata zauna gurin uwarta ba, kuma idan ma ta zauna can zata iya sulalawa ta koma gidan Hajiyar ba tare da saninka, kara tana gabanka kana ganinta, albashi ka samu ko masinja ne cikin ma’aikanta ka aura masa ita mu huta…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected