Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Captain yaja numfashi ya sauke har lokacin yana jin fever dake tare da shi ya kwadayin son abu mai ruwa be fita jikinsa ba.
“Wannan dalilin ne kadai ya saka na dagawa Salim kafa, ta bangaren nan yayi min hallaci kuma mahaifiyarsa ta cancanci ko wane kalar tukuici daga gareni”
“Me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
Hamad ya tambaya, sai dai Captain be kula tambayarsa ba ya dauko zaren labarin tun daga tushe.
“A ranar da na zo gidan nan, na shiga bangaren Momy na samu Hurriya tana kuka ta fada min cewar an dauke dan’uwanta, kamin ita Namra ta ba ni labarin abun da ya faru saboda tana saka ran ko akwai hannuna a ciki ne saboda fasa min tayun mota da Hamad yayi da kuma kyautar da na yi ma Hurriya a lokacin ta gilashi sai ta ki ta karba, na ce mata sai na dauki mataki, a yanayin yadda aka ba ni labarin ma sai na fahimci ba Hamad aka zo dauka ba Hurriya aka so sacewa da ba sameta ba ne aka dauke Hamad, a ranar Hurriya ta roke ni wata alfarma ta tambayi sunana na ce mata ni Soja ne sai tace Malam soja ka nemo min dan’uwana dan Allah, ni kuma na mata alkawarin zan nemo mata shi har na yi mata rubuta a takardar na ranar da na dauki alkawarin da sign na bata, tun daga lokacin sai na baza mutane na neman yaron sai dai ba a same shi ba sai after an yi sanarwar cewar ya mutu a nan, sojojin da suke aiki a hanyar sokoto suka samu gawarsa a cikin wata gona shi ma kuma saboda sun za su shiga cikin kauyen dake gurin ne gurin kai farmaki, a take suka sanar da da headquarters Mu cewar sun samu gawar yaron da na ba da cigiya na shigar da report akansa, su kuma suka sanar min, a take na shirya ni da kaina na tafi gurin tare da wasu soldiers daga headquarter saboda bincikar yadda komai ya faru, sai muka samu har lokacin yana zubar da jini fresh blood ba daskarare ba irin na wanda ya mutu, kuma da na taba shi sai na samu yana da rai amman baya numfashi, a take muka dauki gawarsa zuwa asibitin tureta dake sokoto muka saka likitan gurin ya duba shi sai ya fada mana cewar alama sun nuna yana raye, amman yayi nisan da abu ne mai wahala ya iya tashi saboda ran sa yayi nisa kadan ya rage masa, i never give up na dauke shi daga wannan asibitin zuwa asibitin dake cikin garin sokoto wato asibitin anan suka karbe shi suka yi iya abun da za su iya kuma aka yi nasara numfashinsa ya dawo, sai dai sun fada mana abun ya taba kwakwalwarsa, da ya fara jin sauki sai ya zama be bude ido be cewa komai baya motsi numfashin ne kawai a duk tsawon lokacin nan yana karkashin kulawata ne, ni da kaina na nemi Salim ya taimaka min na je da yaro a kasar da mahaifiyarsa take, saboda mahaifinsa dan garin gusau ne, dan Sarauta Family’s, sai dai mahaifiyarsa yar kasar Ethiopia ce aiki ya kai mahaifinsa a can ya aure suka haifi Salim da Ziaw sai suka rabu ya dawo nan Nigeria tare da Salim ya bar nata Ziaw a can wannan dalilin ne ya saka ke kiran Salim da Ethiopian saboda yana zuwa gurin mahaifiyarsa sosai yana zama a gurinta, be musa min ba ya amince sai na nemi transfer daga asibitin zuwa asibitin Medical Center Hayat MCM, saboda ina tunanin duk wanda zai saka ayi ma karamin yaro kamar Hamad haka zai iya kashe shi idan ya san yana raye, kuma gashi mu ba mu da full evidence na wanda ya aikata hakan balle mu kama shi, tun da ba mutanen aka kama ba gawarsa kawai aka samu, ko ba komai a can kasar zai fi samun kulawa fiye da nan, da Salim muka shirya komai bayan na fada masa halin da ake ciki shi kuma ya sanar da mahaifiyarsa sai ta yi mana duk abun da ya kamata muna isa aka karbeshi a asibitin, kuma sai aka yi sa’a yana ta samun sauki, sai dai hankalinsa ya tabu ya kan yi wasu abubuwan masara dadi yana yawan firgita da kiran sunayen Iyayensa sai likitocin suka tabbatar min da cewar matukar ba a sama masa abun da yake so ba zai iya haukacewa kuma zai yi wahalar warkewa, wannan dalilin ya saka idan na kai masa ziyara ko Ziaw take ko Mahaifiyar Salim mu kan cusa mata cewar bashi da kowa, na kan ce baka da kowa Hamad kai kadai yake rayuwa ko bachi yake idan na fada masa haka sai ya zabura, na fada masa kowa naka ya mutu a yanzu mu wasu Iyalin ne da ka samu wadanda ba ka sani ba, a haka sai da Hamad ya kwashe shekara daya a asibitin sannan ya ji sauki har suka sallame mu, sai na kai shi a gidansu Salim a gidan ya fara rayuwa kuma ya rayu da karyar dana cusa masa cewar ba shi da kowa”
Captain yayi shiru yana jan numfashi kamin ya cigaba.
“Be cika damuwa ya bani labari ko yayi hirar rayuwarsa ta baya ba, wata kila saboda na riga na fada masa cewar ya rasa kowa ba, wata rana ya taba tambaya ya aka yi ya rasa kowa sai na fada masa, yadda na tsince shi, kuma a lokacin da yake nan asibiti ma nemi iyayensa sai na samu bakincikin rashinsa ya kashe su, sai ya tambaye ni ina da wata wata yar’uwa Hurriya ita baka ganta ba? Haka ne Hamad…?”
Captain ya tambaya sai Hamad ya daga masa kai yana tuna lokacin.
“Na ce mishi ita ma na yi mata irin yadda aka yi maka, shin kana sha’awar komawa garin da babu kowa sai yace min aa, da haka na samu ya fuskanci rayuwarsa na saka shi makaranta a can, saboda ya fada min lokacin da yayarsa yake raye yana da burin zama likitan ido saboda ita, na karfafa masa guiwar yin karatun saboda ya cika burinsa, har kai inda yake a yanzu, a lokacin da ya gama high school sai na nema masa makaranta a kasar kuma muka nemi bangaren da yake aka ba mu, saboda sun yaba da hazakarsa, a yau Hamad yana cikin best students na makaranta mai su kwazo da maida hankali, na taba daukar hotunan Hurriya na tafi da su na zimmar nuna masa sai kuma na kasa hakan, saboda ban san ta yadda zan amsa masa tambayar da zai min ba, kuma a lokacin ba ni da kakkafar alaka da ku kamar haka, kuma na san mahaifiyarsa ba zata iya daukar wani mataki ba, tun da ga Hurriya ma a lokacin ana musguna mata babu wanda yace komai na san wanda ta aikata wannan zata samu wanke kanta cikin ruwan sanyi ko ma ta sake kashe shi”
Captain yayi murmushi yana tuna bawa.
“Na bawa Hamad labarin sabuwar budurwar da na yi, har nace mishi ya dauketa a matsayin yayarsa sai ya ba ni abun hannu a matsayin kyauta kuma na kawo miki Hurriya gashi nan a hannunki”
Hurriya ta kalli abun hannun ta kalli Hamad Hamad ma ya kalli abun hannun da ya taba bawa Captain.
“Ta yadda zan juyar da karyar da na yi ta zama gaskiya ne abu mai wahala a gareni, shiyasa na bar abun a haka har zuwa lokacin da gaskiya zata yi halinta, kuma wannan ne dalilin da ya saka na zabi zuwa Ethiopia aikin idon Hurriya fiye da ko wace kasar, lokacin da na yi wacan lafiyar tare da Salim muka tafi a lokacin ya gane ina son Hurriya hakan yasa har yanzu nake kyautata zaton shi ya yada hotunan Hurriya a kafofin sada zumunta, kuma zatona ya tabbata domin hacking din da na saka ka yi min da kuma bincike sirrin wanda na saka aikin ya fada min haka, sai dai yadda ya samu hotunan ne abun da ya daure min kai, a lokacin da yayi min furucin cewar yana da sauran amfani a gurina sai na saka aka dauke ka daga gidansu aka kama mata masauki a makarantarku saboda gudun kar zuciya ta saka shi ya cutar da kai, na san akwai tsaro a makarantar ta yadda ko da ya aikata maka hakan za gane ko waye…”