Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Wake da dadin zuciya a yanzu Khairy? Ai sai idan abubuwa sun daidaita, ni kaina yanzu abincin kirki bana iya zaunawa na ci, abubuwa sun hade min? Ga sakin nan da Alhaji yayi min ko waiwaye gefena be sake yi ba, kamar wanda ya aje kashi… Ga Iyami a gafe damuwarta na son yi min yawa, yanzu ga Hurriya da gani magani suka yi ma yaron nan suka aura mata shi, kauyen nan kuma mun je mun tararda bakin labari, ban da ma karfin zuciya ai sai mutum yayi mutuwar tsaye ko ta gaba daya a take”
“Hajiya wannan duk saboda Amma ne, ita ta haifi Hurriya har ta kawo mana matsala a gida”
Hajiya ta hade hannu biyu ta daga sama.
“Saboda ita ne kuwa saboda ita ne, ni ko mutuwar Salma ai bana raba dayan biyu da laifinta a ciki, ga kamun da barayi suna yi mana shekarun baya saboda ita ne dai, ni kam yau da zan ga Iyami ai da hannuna zan kashe ta, duba ki ga Hurriya waya auri irin mijin da ta aura a yanzu? Duk cikin yayan Alhaji babu wanda yayi dacen miji irinta duk bayan cin amanar da ta yi min”
Maganar take zuciyarta na zafi sosai saboda bakinciki, kamin su dago kai su kalli juna jin tsayarwa mota har biyu a bangaren ana rufe gambun da karfi. Khairy ta tashi ta leka windows din Falon dake bawa mutum damar hango abun da ke waje, a take gabanta ya yanke ya fadi.
“Appa ne tare da Yaya kuma nan suka nufo?”
Ta saki curtains din ta dawo kusa da Hajiya Kaltume ta zauna zuciyarta da jikinta na rawa, Hajiya Kaltume ta maida hankalinta gurin kofar tana tunanin abun da ta yi domin a yanzu bata da tabbacin alheri zai kawo mijinta a bangarenta. Yasir ne ya fara turo kofar falon ya shigo sannan Appa ya biyo bayansa. Daga Khairy har Hajiya Kaltume faduwar gaba suka samu kansu har Appa ya zauna yadda Yasir yake karara Khairy ita kanta ta san akwai wani abu a kasa. Hajiya na son tambayar lafiya tana jin tsoron domin ta lura da yanayin Appa ba yanayi mai kyau ba, sai da ta dubi Yasir sannan ta kalli Khairy da yake harara.
“Wani abun kika yi?”
Khairy ta yi shiru jikinta ya hau kyarma zuciyarta na zillo.
“Umm Khairy… Me kike aikatawa Hurriya?”
Ras ras ras gabanta ya fadi irin faduwar da be taba yi ba, sai ta kasa amsawa kuma ta kasa daina kallon Appa fuskarta kuma ta kasa boye tsoronta.
“Me kike aikata ga Hurriya?”
Appa ya sake tambaya yana kallonta. Yasir ya mike tsaye zai nufi inda take sai Appa ya dakatar da shi.
“Dakata, ba abu ne na duka ba, wannan abun mai muni duka ba zai canja komai ba, ni kadai na san ya nake ji a raina, yaya ne dukansu ace ďaya ta aikatawa ďaya haka? Ya kamata na tambayi kaina me na yi?”
“Baka yi komai ba Appa babu ta inda ka gaza, dan Allah karka sakawa kanka tunanin wani abu”
Yasir yayi saurin fada yana kokarin kwnatarwa mahaifinsa da hankali. Hajiya Kaltume ta kallesu ta sake duban Khairy sannan ta ce.
“Duk lokacin da za’ayi ma Khairy hukunci a gidan nan ko duka saboda Hurriya ake mata shi yanzu kuma me aka ce ta yi?”
Yasir ya bude wayarsa ya kunna video ya mikawa Hajiya Kaltume, tana fara kallo Khairy ta fara hawaye domin ita ma tana jin abun da ake fada, sai ga Hajiya Kaltume rike da baki.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un sherin sa za’ayi ma Khairy kenan?”
Appa ya nuna ta da tsaya.
“Ban shigo nan falon na zauna dan na yi magana da ke ba, karki kuskura saka min baki a magana, duk wata asalin kiyayya da tsana da neman ganin baya ko kunyata wani daga gurinki ta samu asali, duk abun da Khairy ta aikatawa Hurriya a yau goyon bayanki ne rainonki ne, ke kika bude musu hanya ke kika nuna mata hakan, kin tsani yarinyar nan kin tsani uwarta, akan abun da Allah be haramta ba, kaina farau aure? Da a gidana kawai za a samu wannan tashin hankali? Ke ya kamata ki hada kan yaya matsayinki na uwar gida amman baki yi ba, sai dai ki nuna musu tsana da banbanci, yau duk wannan abun ya faru saboda ke ne!”
Ya maida dubansa gurin Khairy dake kuka.
“So nake ki karya ki banranta kanki kamar yadda Hurriya ta yi min rantsuwa bata aikata ba”
Ta girgiza kai tana saukowa daga kan kujera tana kuka. Yasir ta dafe kansa ya runtse ido sosai.
“Tir da halinki…! Tir da haihuwar ƴa irin… Tir da ke Khairy ba zaki taba ganin abun da kike so ba a rayuwarki…. Taya zaki hada kai da wani namijin a waje saboda cin ma burinsa ga yar’uwarki ta jini? Ki taimaka masa ya gaya rigar mutuncinta? Ko kawarki bata cancanci haka a gareki ba balle kuma Hurriya, karshenta gashi ya fadi abun da yayi miki hakan kuma be miki ba sai da kika yada hotunanta a duniya…”
“Na ji… Ni na hada kai da shi aka dauki hotunanta… Wannan gaskiya ne amman Wallahi Tallahi ba ni na yada ba, ban yadawa duniya hotunan Hurriya ba, Wallahi ban saka hotunanta a internet ba, bayan Adam ban turawa kowa ba Wallahi, akan wannan zan iya rantsuwa da kur’ane, sheri ne kawai yayi min”
“Amman kin karbi kudinsa da sunan zaki nema masa hadin kan Hurriya? Ta yadda zai samu damar Lalata da ita?”
Appa ya tambaya hopping to hear NO from her. Ta hade hannayenta tana kuka sosai.
“Na aikata… Ka yafe min Appa ka yafe min dan Allah? Dan darajar Hajiya… Ban aikata hakan saboda na kunyata ku ba, ban yada hotunan ba…”
“Lahaula wala kuwwata illabillah, Khairy karki kuskura ambatar sunana a gaban kowa daga yau, kar wata matsala ko matsi da kunci ya saka ki tuna cewar ni mahaifinki ne….”
Hajiya Kaltume ta saka Kalma shahada Yasir ya kalleshi da sauri Khairy kuma ta fashe da kuka mai karfi ta je ta gudu ta kama kafar Appa da tuni ya mike tsaye ya fara tafiya bayan ya fadi hakan.
“Appa ka yafe min dan Allah, na tuba ka yi hakuri dan Allah… Ka yafe min Appa”
Tsayawa yayi ya kasa tafiya kuma ya ji ba zai iya juyo ya kalleta ba saboda ta bata masa rai matuka.
“Bana bukatar ganinki”
Ya fisge kafarsa ya fice daga falon ya barta a gurin tana rusar kuka. Ta juya gurin Yayanta.
“Yaya Yayaya… Dan Allah ka bawa Appa hakuri dan Allah…. Wallahi Wallahi ba ni na yada ba… Sheri yayi min saboda ya hada ni da mutane ba ni na yada ba”
“Ko sa yaushe idan na yi magana akan abun da yarinyar nan take yi cewa kike ina matsawa yanzu ga abun da ta haifar, wani ya keta mutuncinki a banza kuma yanzu za a yada hoton siraicinki… Kamin mu shigo nan Appa kuka yake da idonsa miye amfanin ya ta saka ta mahaifinta kukan bakinciki? Miye ribar hakan?”
Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya fice yana kuka. Hajiya Kaltume ta mike tsaye tana kuka ta nufi gurin da yarta take kwance a kasa tana mulmula ta rikata cike da tausayinta.
“Ya yanke hukunci ne cikin fushi, ki yi hakuri Khairy zai sauko…”
Ta fara share mata hawayenta tana nata kukan.
“Amman da gaske yaron nan yayi miki fyade?”
Khairy ta daga kai wani sabon kuka na zuwa mata.
“Shiya hana ni farinciki da sakewa tun daga ranar har yau… Hajiya ashe haka ake ji idan aka yi ma mace fyade….? Bakincikin abun ya fi na mutuwa…”
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un….”
Hajiya Kaltume ta fashe da kuka ta rumgune yarta.
“Ba a bar maganar nan ba, Allah ya isar miki ba zan kyale yaron nan ba… Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un wannan masifa ta mana yawa…!”
*** *** ***
Tsaye Appa yayi a dakinsa ya rumgume hannayensa a baya yana kallon sama. Fuskarsa da zuciyarsa babu komai a cikinta sai tarin damuwa da bakinciki, kokarin yake ya gano wani kuskuren da ya aikata har aka jarabce shi da wannan, wani abun kaddara ce kai tsaye domin gwada imanin bawa da zuciyar ko tana iya dauka, wani abun kuma ishara ce na wanin abun da aka aikata daidai ba ko kuma a can baya. Ya nemi guri ya zauna sai kuma ya ji kamar ya zauna a ruwa saboda damuwar da yake ciki hakan ya saka shi mikawa tsaye ya fara zagaya dakin. A yanzu ya gane tun farko yayi kuskure be tsaya ya zabe uwar da ta dace da yayansa ba, be duba dabi’u da hallaya ba, be duba mai addini ba kamar yadda Annabi ya koyar, duk ya tsallake wannan gashi yanzu dafin abun ya bibiyeshi. A dakin yayi sallah Azahar saboda jikinsa da yake jin ya sauya masa kamar ba na shi ba, wani abu mai kamar zazzabi yana rufe shi, zuciyarsa na ciwo sosai. Bayan yayi Sallah ne ya dauki wayarsa ya kira direbansa ya fada masa ya kimtsa mota za su fita yanzu, sai da ya mike tsaye sai jiri ya debi shi ya fadi kasa zaune yana ambaton Allah, can kuma ya sake yunkurawa ya mike tsaye sai gabansa ya rike kirjinsa yayi kamar an tokare shi da mashi, a nan sai da yayi ta addu’a sannan ya samu abun ya sassauta masa, a lokacin da ya fito ya shiga motarsa sai ya ji baya bukatar kallon bangaren Hajiya Kaltume domin ji yake kamar ita ta aikata haka ba Khairy ba, wani bangaren kuma yana ganin kamar da hadin bakinta, a yanzu ne yake mamakin kansa da be karasa mata igiyar da ta rage a tsakaninsu ba, ya kamata ya kabe ta daga gidansa ma gaba daya, sai a yanzu ne yake kara jin tsanar ta irin tsanar da be taba ji ba, nadamar shekarun da ya bata a tare da ita yake a yanzu, arzikinta ďaya yaran dake tsakaninsu ba dan haka ba shi kam da ko sunanta a yanzu ba zai sake son a ambata a gabansa ba. Har ya isa garin Maradum be ya tunanin komai sai irin zaman rashin ji dadi da Hajiya Kaltume ta yi da uwargidansa wato matarsa ta farko Maryamu uwar Sapna, an yi zaman da babu dadi ga fitina da tashin hankali kuma mafi akasari daga gurin Kaltume yake tasowa, kasancewar Allah ya saka zaman ba mai tsawo ba ne sai Maryamu ta bar mata duniyar.