Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un”
Shi ne abun da Amma ta iya furta idonta na cika da hawaye, furucinta yayi sanadin tashin Hurriya daga bachi ta tashi zaune da sauri ta gyara zaman gilashin idonta tana kallonsu. Gwaggo da Rukayya suka iso gurin suna jin abun da ya faru kowa ya dora hannu saman kai, Gwaggo ta daki kirji.
“Miliyan dari dari?”
“Eh shiyasa Hajiya tace ita dai zata bada abun da yake hannunta Appa ya hada ya karbo mata Ruma, domim shi Appa so yake sai ya tsaya ciniki da su, ita kuma ta ce ita kadai ta san azabar da ta sha, mutane ba su da imani”
“Miliyan dari biyu be fi karfin Alhaji ba, rayuwarsu ta fi kudin amfani idan ma kyashin badawa yake ji ni ma zan hada abun da nake da shi na ba shi, ni dai a dawo min da yarona rayuwar yarona ta fi min komai, dan Allah ki karbo min number da suka kira a hannun Alhaji zan kira na yi magana da su”
“Toh”
Bata wani dade ba ta tashi ta fice ta bar Amma da Hurriya suna ta kuka. Sai da ta fita sannan Gwaggo ta kalli Amma ta ce.
“Allah masani, amman anya babu sa hannun Hajiya Kaltume a lamarin nan? Akan me zata nuna miki ki hada kudin da yake hannunki ki bada?”
Amma ta kalli Gwaggo tana hawaye ta ce.
“Wannan rashin imanin yayi yawa, Hajiya ba zata iya aikata haka ba, idan ma zata aikata ba zata aikata tare da yarta ba, ni dai zan gada komai nawa na bada dan Allah Gwaggo karki hana ni”
“Duk da haka dai, ki saurara har ki ji ta bakin Alhaji Haruna din, zan saka Bappanku ya kira shi yayi magana da shi ko ma yaje ya same shi mu ji yadda ake ciki”
“Appan Hurriya yana da kafewa wani lokaci ni ba zan iya jira har lokacin da zai karbo su ba, Allah kadai ya san halin da Hamad yake ciki”
“Toh ke yanzu ina kika ga miliyan dari Iyami?”
“Ba za a rasa ba Gwaggo ko kudin be kai ba, akwai kaddara”
Amma na fada tana kuka ji tana kamar ta tashi yanzu yanzu ta gada kudin ta mika musu su sako mata Hamad.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
@
Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660
3️⃣
Tun a ranar Bappa ya so ya samu Appa su tattauna kan lamarin amman hakan be samu ba sakamakon dare da yayi, daman daf da magariba Maama taje gidan. The following the day Bappa yayi ta kiran Appa a waya amman yaki dagawa, cikin yanayin damuwa Bappa ya kalli Iyami dake rike da carbi ya ce.
“Haka nake da bawan Allah nan, babu ranar da zan kira shi ya amsa min, tun da lamarin nan ya faru idan na kira shi baya daga wayata”
“Wata kila har yanzu yana jin kunyarka ne, ina ganin abun da zai fi ka shirya ka same shi gida da safen nan da wuri sai ka yi magana da shi”
“Ko kuma ita Iyamin ta kira shi a wayarta ba, ta yi magana da shi ko kuma ta ba ni wayar mu yi magana”
Ya karasa yana kallon Amma. Amma ta dauki wayarta ta lalabo number Appa da rabon ta yi waya da shi tun tana gidan, kamin ta danna masa kira ma sai da ta yi da gaske ta danne zuciyarta, sanin cewar saboda matsalar Hamad zata kira shi ya karfafa mata guiwar kiran, sai ita ma ta yi rashin sa’a kamar Bappa, be daga kiran ba, tun kiran na ringing har ta kai an fara rejecting.
“To wai lafiya ko kuma dai yana tsoron kar a fada miki ne, wata kila be san Maama ta zo gidan nan ba, ina tunanin a boye ta zo ta fada miki, domin irin wannan magana mai nauyi shi ya kamata ya taho da kansa ya fada miki, anya ba Hajiya Kaltume ta taro ta ba?”
A take Bappa ya gwatsale Gwaggo daman shi be cika yarda da irin abubuwan nan na zafin kishi ba, ko wani abun da za ace kishiya ta aikata ganin yake duk karya ne, ko wane bangaren daman ba zai so dayan bangaren ba dan haka kazafi da kage babu kalar wanda ba zai yi ma abokin adawarsa ba.
“Ku dai kullum baku da wata magana sai ta Hajiya Kaltume, ina ce saboda Hajiya Kaltume nan Iyami ta hadu da Alhaji, ni fa a gurina bani da kamar Hajiya Kaltume domin sanadinta Iyami ta auri Alhaji Haruna Mai Yadi, idan na fita har nuna ni ake ga surukin Alhaji, da can ba a kwano muke zaune ba? Amman ya zo ya siya mana babban gida ga kuma lalurar komai ya dauke mana, duk sanadin waye ba Hajiya Kaltume me? Dan Allah ku daina kawo min maganarta ma”
Gwaggo ta rausayar da kai.
“Toh Malam ai daman ba zaka yarda ba, baka san makircin mata ba”
“Ban sani ba, kuma bana son sani, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi tare can mu same shi mu yi magana da shi”
“Toh bari na dafawa Hurriya Indome ta fi son karyawa da ita”
Amma dai bata ce komai ba, har suka ci suka shude, ita dai tunaninta na halin da danta yake ciki ne. Sai da Gwaggo ta dafawa jikarta Indomie ta zuba mata a karamar cooler sannan ta yi wanka Bappa ma yayi wanka suka shirya sannan suka bar gidan.
MAI YADI’S HOUSE.
Hajiya Kaltume ta dan leki wayar da Appa ya aje a gefe daya ta kalleshi.
“Iyami ce fa Alhaji?”
Appa kamar wanda aka rikita sai ya fara fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba.
“To me zan mata? Ba za a bar mutum da damuwarsa ba? Ta san halin da nake ciki ne? Mahaifinta yanzu ya gama kirana ita kuma ta dora da nata”
A kaikace Hajiya Kaltume ta ce.
“Ka sani ko zancen dawowarta za su maka ko kuma na Hamad?”
“Dawowarta? Ta zo ta yi me? Hamad kuma ai ni ma dana ne ba ita kadai ta haife shi ba balle ta nuna min sonsa”
“Gaskiya kam, ni ma da aka dauke min Ruma ai dole na zuba ido sai abun da ka yi, amman duk da haka dai Alhaji da dai ka bada kudin”
Appa yayi shiru kamar mai tsoron musa mata, ya kasa cewa komai.
“Kuma ba ka san shakkuwarta ba, da ka karba wayar ka ji abun da za su fada”
“Bana son na ji wani abun da da ya shafi Iyami ko gidansu a yanzu, damuwa ta min yawa kaina ma kamar ya fashe nake ji, na san kuma damu za su yi da maganar Hamad”
“Ikon Allah yau Alhaji Iyamin ce baka son jin wani abun da ya shafe ta? Toh Allah ya kyauta bari na kwashe kayan”
Ta fara kwashe kayan da ya ci abinci zuciyarta na wani irin zillo kamar zata fado tsabar farinciki. Jikinta har rawa yake kamin ta bar part din, tana shiga bangarenta ta aje tray a falo ta shige dakinta ta dauki wayarta sai kira ta aikawa Hajiya Fatee.