Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Gafen fuskarta ya hau zugi yayi ja, idanuwanta suka masa tantance mutunen da ke tsaye a gabanta, fafadane ta ga hakan a cikin hudun idanuwanta, dogo ne irin tsayin da ta tsaya iyakar kirjinsa. A hankali ta sulale ta kai kasa ta saka hannayenta tana lalaben gilashinta hawaye na kwankwaso mata kofa. Lalabe ta yi ta yi amman ta kasa jin gilashin, kamar yadda ta duka haka ta mike tsaye a hankali ta juya ta lalabi kofar falon ta fara tafiya.
“Hurriya… Me ya same ki”
Namra ta tambaya tana nufota da sauri ta kama hannayenta ta rike domin hawaye take kamar an bude kofar fanfo.
“Ya… Ya… Namra… Gilashi… Na…”
Namra bata tsaya komai ba ta rika hannunta ta juya da ita suka fita tana janye da hannunta, har lokacin Mutumen da ya mareta yana a gurin tsaye ko yatsansa be motsa ba. Namra ta kalleshi kamin ta sako hannun Hurriya ta fara duba gilashin, can gefe ta hango shi ta nufi gurin da sauri ta dauko mata.
“Har gefen ido daya ya fashe daga sama, me ya faru Hurriya”
Ta saka mata gilashin da kanta, lokaci daya ganinta ya dawo fashewar da gilashin yayi ba irin wadda zai hanata gani ba ne, daga sama ne ya fashe shi ma kuma kadan. Hurriya ta daga ido ta kalli mutumen da be mata uzuri ba ya wanke fuskarta mai tsada da mari. Hawaye be daina mata zuba ba, hakan kuma be hana idanuwanta ganin mutumen da kyau, dubansa ta yi ta dube shi, ta sake dubansa sannan ta sauke idonta kasa ta ratsa gefensa ta fara sauka kasa. Slowly ya juya ya kalleta kamar mai son gasgata wani abu ko karyatawa.
“Bata gani sai da gilashi, me ya faru Yaya?”
Ya juyo ya kalli Namra a fusace.
“Aza min bindiga sai na fada miki”
Jinin jikinta ta sha ta kauce ta ba shi hanya ya shiga ciki, ita kuma ta ja kofar sannan ta bi bayan Hurriya domin gaishe da Hajiya Binta, kamar yadda Appa ya sabarwa kowa a gidan ko baka cikin gidan idan mahaifiyarsa ta zo matukar kana cikin garin sai ka zo ka gaisheta…
☆❁ ❁☆
Hello Habibaties
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy
https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy
1️⃣1️⃣
Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan.
“Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa”
Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta.
“Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni”
“Me kika masa?”
“Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai”
Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba.
“Ina yake?”
“Yana bangaren Momy”
Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna.
“Kalli abun da ka yi”
Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba.
“Allah ya kyauta”
Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar ďanta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi.
“Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho”
Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa.
“Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki”
“Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo”
Appa yayi murmushi.
“Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana”
Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi.
“Me ya sami gilashinki Hurriya?”
“Faduwa na yi”
Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce
“Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba”
Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa.
“Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba?”
Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi.
“Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah”
“Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana musguna musu kamar wasu ba yi, har dokoki ake saka musu a gida, kuma duk tarin masu aikin gidan nan ace Hurriya sai ta share dakinta da na Hamad su sauran yaran ai ba haka take musu ba, shiyasa tun a lokacin da na ji ka saki Iyami na kira Nafisa da Kaltume na ja musu kunne akan yaran nan ashe na yi a banza, da Iyami ce ko ba zata jefar da magana ta ba”
“Za a gyara Hajiya, amman dan Allah ki aje maganar daukarsu ko maida su gurinki, tun da Iyami ta bar gudan nan yaran nan kawai nake gani ina jin sanyi, idan kika dauke su karin wata damuwar ne a gareni”
Hamad ne ya shigo falon rike da karamar wuka a hannu ya zauna kusa da Hajiya Binta ya aje wukar gefe.
“Me ya hadaka da wuka Hamad?”
“Apple na yanka”
Ya amsa tare da daukar spoon ya saka a abinci da Hurriya ta zuba.
“Hamad abinci Hajiya ne fa kana ganin na saka nama da yawa shi ne kuma zaka saka spoon”
A take ya daka mata tsawa.
“Toh ina ruwanki da ni, ba zaki daina shiga min hanci ba ko? Hajiyar ta ki ce ke kadai”
Hurriya ta kalli Hajiya tana turo baki alamar ta fusata.
“Hajiya kin gani ko?”
“Kyale shi zuba mana wani”
Hamad yayi kwafa, Hurriya ma ta yi kwafa daman tana da haushin marin da aka yi mata zuginsa be gama wucewa a kuncinta ba. Ai a take Hamad ya daga hannu zai kai mata duka Appa yayi saurin rikewa.
“Kai Kai Kai Kul daga magana sai ka ce zaka duketa, ita ce yayarka fa, ba zan daukar maka wannan ba Hamad, haka Iyami ke ta fama da kai kai baka san ka ragawa kowa ba?”
“Amman Appa ai ita ta fara”
“Yi mata hakuri kyaleta ai yar’uwarka ce baka da kamar ta, kyaleta”
Ba dan kakarsa Hajiya Binta ta saka baki ba zai bar Hurriya ta zauna lafiya ba, hakan kuma be hana shi sake yin kwafa ba sannan ya fara cin abinci.
“Ni wannan zuciya ta Hamad ban san gun da daukota ba, fushinsa har tsoro yake ba ni”
Appa ya fada yana shafa kan dansa, Hajiya ta ce.
“Zai daina kurciya ce, da zarar ya girma ya mallaki hankalin kansa zai daina, wani lokacin yara idan suna jin tashin balaga haka suke jin kamar daidai suke da kowa, ka bar shi ya cike 20 ko 18 fushin nan duk zai hauka”
“Allah yasa, ya shirya mana”
Hajiya ta amsa da Ameen. Sai da suka gama cin abinci sannan Hajiya ta tashi tare da jikokinta Hamad da Hurriya Appa na gafenta suka fito daga bangaren na Appa zuwa bangaren Hajiya Kaltume domin yi mata jaja da kuma barka da kubuta. Ko da suka shigo falon na Hajiya Kaltume yana cike da yayanta da kuma yayan yan’uwanta da ma ita kanta sai hira ake har da Namra. Kamar ta Allah haka Hajiya Kaltume ta washe baki tana maraba da zuwan Hajiya Binta.