VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Appa bana ganin komai yanzu, bana ganin komai sai abun da ya faru, me yasa suka dauke Hamad? Me yayi musu?”

“Wallahi dukanmu ba su sani ba, amman dai an san ba zai wuce su ce a ba su kudi ba, kamar yadda suka yi ma Kaltume kuma shi ma za su sako shi”

“Hadda Ruma aka kama”

“Na sani duka zamu biya kudi mu karbo su Da yardar Allah, amman yanzu zamu tafi dake gurin police za su miki tambayoyi akan abun da ya faru, saboda kun sanar da ya sanda, kamin nan kuma ina son ki min alkawarin ba zaki fadawa Iyami ba, kuma ki daina kukan nan har sai mun karbo shi”

Kamin Hurriyya ta dauki alkawarin suka jiyo Amma daga jikin curtains din kofar dakin tana furta.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un.
Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un
Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un”

Daga Appa har Hurriya ba su san Amma ta yi labe ba sai a lokacin. Appa ya taso ya fito da sauri yayinda Gwaggo ma ta fito da sauri daga dakin Amma ta nufota.

“Gwaggo sun dauke min Hamad, su biyu Allah ya ba ni sun dauke daya, kashe shi za su yi Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Gwaggo ma ambaton Allah ta shiga yi tare da rike Amma dake shirin faduwa.

“Allah yasa kaddara ba musanya zata min ba, Allah yasa ba Hamad za a dauke a ba ni wani ba, La’ilaha Illallahu, Allah kasa kari zan samu ba musanya ko ragi ba, su wa suka dauke shi? Na san ďana be jin magana amman su yi hakuri dan Allah idan wani laifin yayi, kowa ya min haka be kyauta min ba, me suke so Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un”

Gwaggo ma sai da ta fashe da kuka saboda kukan da Amma take yi. Appa kuma yayi tsaye a gurin hopeless yana kallon tsohuwar matarsa dake dauke da cikinsa ya rasa me zai yi.

 

Littafin nan kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

________________

https://chat.whatsapp.com/F1ch00M9VNvFxrVVgCEeXo

Ina Yan uwan Yan gayu makotan Masu Kudi?
Daku nake Magana.
Matan da suka san ciyon kansu masu hada goma ta zamo ishirin kuzo ku sari Kaya acikin sauki da rahusa a Ummu Ahmad store muna kawo kayan mu ne daga Lagos masu quality da karancen farashi akwai kayan kitchen akwai shoes and bags, Akwai kayan abinci na awo laces,kayan yara,da sauransu
Sannan akwai kayan gyara irin su tsimi kala kala gumbar mata daban daban maganin sanyi
Akwai kaza me rubutu da wadda akeyi da sanyun magani
Akwai taimako na haihuwa ga wadda taje asibiti akace batada matsalar komai akwai rubutun da muke badawa Wanda idan ta gama Al adarta zatayi amfani dashi za adace da yardar Allah
Akwai kayan kamshin daki da na jiki

Location dinmu zamfara
Muna tura Kaya a koina kk cikin aminci da yardar Allah payment validate ur order Ummu Ahmad 08032350261

Ni Khadeeja Candy nake tabbatar muku ba zaku taba nadamar siyen kayan Little Mommy na ba, uwata ce ta jini ba lake lake ba, please patronize her tana siyar kaya masu kyau da imganci, zaku iya tuntubarta ko ma ku tuntube ni kai tsaye sai ku zo

@

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

2️⃣

Sai da Gwaggo da Mama Rukayya suka yi da gaske sannan suka iya rarashin Amma ta yi shiru, suka dagata suka shigar da ita falon har lokacin Appa ya tsaye ya rasa abun cewa, Hurriya ma kuka take sosai tana tausayin kanenta tana tausayin mahaifiyarta.

“Dan Allah Gwaggo a kwantar mata da hankali, ba yau aka saba daukar mutane kuma ana dawowa da su lafiya, na san dai ba zai wuce su ce suna bukatar kudi ba, kuma ba mu biya mu karbo shi”

“Toh Allah ya bayyana shi cikin aminci”

Gwaggo ta fada cikin kuka, sai a lokacin Appa ya samu courage din fice daga cikin gidan tare da Hurriya, a mota ma Appa ya wahala kamin ya samu Hurriya ta yi shiru, hankalinsa be kara tashi ba sai a lokacin da take bada labarin yadda abub faru. Duk wani abu da ya kamata su tambayeta sun tambaya kuma ta ba su amsa sannan Appa ya dauko ta a motarsa tare da Direbansa suka nufo gida.

“Appa ka kar ni a gurin Amma please bana son nan”

“Zan maida ke can Hurriya, ita ma ai ganinki zai saka ta dan ji sanyi, zaki dauki tufafinki, sai kuma Yasir ya baki dayan glass dinki da yake can”

“Toh”

Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa gidan. A harabar Momy Appa ya umarci direban ya faka, sannan ya fito direban ma ya fito da sauri ya budewa Hurriya mota Appa ya rikata ta fito, suka nufi bangaren ransa a jagule gaba daya shekarar nan ta zo masa a yadda be yi zato ba. A hankali ya tura kofar falon Momy sai da ya fara shiga sannan ya rikota ta shigo. Captain dake zaune ya mike tsaye yana amsa sallamar Appa, Appa ya karaso cikin falon cikin yanayin dake nuna yana cikin tsananin damuwa.

“Momy bata nan”

“Oh to ina taje? Ina zuwa Hurriya”

Ya saki hannunta ya juya ya fice daga falon.

“Ance kananki?”

Captain ya furta a hankali yana kallon kwayar idonta dake ta juyawa alamar bata ganin komai. Kamar ya tsikaro mata allurar kuka sai ta fara hawaye tana rawar murya.

“A yadda Namra ta fada min ke suka zo dauka, kin san su waye?”

Ta girgiza kai.

“Waye kai?”

Ta tambaya domin bata wayanci ko waye ba. Yayi shiru yana juya invitation card din dake hannunsa for some seconds.

“Soja ne…!”

Ta mika hannu ta fara lalaben inda take jin sautin muryarsa.

“Dan Allah zaka nemo min kanena?”

Tana daf da taba fuskarsa ya kawar da fuskar ya kai hannunsa ya rika hannunta, ba tare da ya amsa mata da eh ko aa ba.

“Dan Allah ka nemo min kanena idan zaka iya, shi ne farincikinmu, shi yake tare min fada dan Allah ka taimaka Malam Soja ka nemo min shi”

Yayi shiru har lokacin be ce komai ba ya saki hannunta daman ya rika hannun ne kawai a kokarinsa na kawaicewa taba fuskarsa. Shi dai abun da ya kawo shi gidan dabam ya zo ya tararda wannan tashin hankali.

“Malam Soja…”

Jin shiru kamar babu kowa a gurin. Sai ya kai hannunsa ya rika 5 fingers dinta ya matsa a hankali domin tabbatar mata yana tsaye a gabanta har lokacin.

“Dan Allah ka nemo min kanena, ku ne sojoji ai ku kuke kama masu aikin yan ta’adda”

Kallon fuskarta yake kamar ance masa tana ganinsa.

“Dan Allah ka taimaka mana, Appa na kudi zai iya ba ku please”

Ya sake rika 5 fingers dinta ya matsa hannunta.

“Idan ka min alkawari ka matsa sau biyu…”

It take him ten seconds kamin ya sake matsa 5 fingers dinta for the third time, sannan ya saki hannunta ya zari Invitation card daya a cikin wadanda suke dayan hannunsa na dama, ya dora su akan mini table dake kusurwar kujerar ya juya bayan dayan card din ya yaga ya ciro pen dinsa yayi rubutu akai sannan ya maida pen din ya sake barkar takardar ya kama hannunta ya danka mata rabin.

“Karki fadawa kowa, kuma karki taba jefar da wannan takardar matukar ina fatar Kanenki ya dawo”

Ta jimke yar ficikar takardar a hannunta tana sauraren takun tafiyarsa har ta ji lokacin da ya bude kofar falon ya rufe. Bayan kamar minti biyar tana tsaye a gurin aka sake bude kofar falon aka shigo.

“Hurriya Appa ya ce na zo dake”

Yasir ta karaso ya rika hannunta yaja suka fita daga falon.

“Na duba ko’ina ban ga gilashinki, zamu je asibiti a siya miki wani yanzu kamin a ga wadancan”

“Ya Yasir yaya zai dawo ko?”

“In Shaa Allah”

Yasir ne ya kaita asibitin gurin likitan da ya saba dubata, suka bata wani gilashin da ya dace da idonta, sai dai idon nata sun sake samun matsala ko da ta saka gilashin bata iya gani da kyau kamar da, hakan ya saka likitan ya sake duba idonta kamin ya rufe ta fada da kuma Yasir wai an barta ta yi kuka mai karfi da yawa har yana son tana gilashin idonta, daman idon lafiya be ishe shi ba. Magani ya bata wadanda zata shafa a idon safe da kuma dare idan zata kwanta sannan ya bata wanda zata diga a idon kamin ta kwanta. Sannan suka dawo gida, kusan duk wanda ya kalleta ita yake tausayawa domin ita ce bata da uwa a gidan kuma ita ce kadai take da kane daya, Hankalin Hurriya be kara tashi ba sai da ta zo zata dauki tufafinta da suke bangaren Momy ta kalli dakin Hamad sai sabon kuka ya taso mata, tana ganin kamar mutuwa yayi ya barsu. Ta saka tufafin da zata iya diba a jaka, ta fito tana kuka ta fice daga falon Momy. Momy dake aikin duba invitation card din da ta tarar a falonta ko kallo gurin da Hurriya take bata yi ba sai yana katin take, Namra ta tashi ta bi bayan Hurriya ta rakata har gurin motar Appa, domim shi yace zai kaita gurin Amma da kansa, sakamakon kiransa da Hajiya Binta ta yi ta ce ya zo ya dauketa ya kaita gurin Amma kuma ya kawo mata Hurriya. Namra ma sai da ta yi kuka saboda yadda Hurriya take ta kuka. Sai da suka fice sannan Namra ta dawo bangarensu tana share hawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected