Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hurriya ta fara waige waige.
“Ina twins din suke?”
“Suna can tare da Yasir, suna ganinshi suka bishi, muje ki raka ni na yi gaisuwar na koma”
Hurriya ta bita suka taka har bangaren Hajiya Kaltume dake cike da mutane ta ko’ina domin wannan ne karo na farko da aka yi mata mutuwa mai nauyi, yan’uwa har nasa sun zo saboda sun san mai hali take aure kowa binta yake sau da kafa a familynsu. Hurriya bata san Hajiya Binta ta zo ba sai da ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da sauri Hurriya ta karasa kusa da ita ta zauna tana gaisheta. Hajiya ta amsa da dan murmushi kadan.
“Hurriya tun dazun nake dubawa ban ganki, na ce kina can kin boya ko sarkin tsoron mutane”
Hurriya ta share hawayen da suka zubo mata ta ce.
“Hajiya Salma ta tafi”
“To ya aka iya, sai hakuri haka rayuwarma zata kare, shiyasa ake son mutum ya ji tsoron Allah ya bawa kansa lafiya, duniya ba gurin zama ba”
Yan’uwan Appa dake kusa da ita suka amsa da cewar haka ne, suna dorawa da nasu sannan suka yi ma Hurriya ya hakuri ta amsa tana kuka kai kace Salma wani kaunarta take. Rukkayya ma ta gaishe da Hajiya Binta sannan suka haura sama tare da Hurriya suka shiga har cikin dakin Hajiya Kaltume, zaune suka sameta kan karamin Carpet Khairy na kwance a cinyarta, kallo daya zaka yi mata ka san mutuwar nan ta taba ba, ba karamin tabawa ba, domin ta fada a take ga ido ya kumbura kamar ya silala, har bata iya daga ta duba mutane da kyau, Khairy ma nata idon ba baya ba domin ta sha kukan da bata taba yi ba, Maama na zaune kan gadon Hajiya Kaltume ita ma kana ganin nata idon zaka san an yi rashi a familyn.
Rukayyah ta mika gaisuwa aka rasa mai amsa mata daga Hajiyar har Maama da Khairy, sai wasu yan’uwan Hajiyar ne suka amsa ta fara gaisuwa tana Allah ya jikanta suna amsawa da Ameen. Hajiya Kaltume ta dago wasu hawayen na zubo mata bakincikin rasa yarta na dawo mata farko, ganin Rukayya da ta yi, da yanzu su ne da kuka ba ita ba, amman gashi nan reshe ya juye da mujiya.
“Rukkaya karki sake shigowa gidan nan, munafurci ya kawo ki saboda ki zo ki ga zan yi tun da na rasa yata, kun jidadi ko? Azzaluman mutane, tun da Iyami ta auri Alhaji ba ni da kwanciyar hankali, kum bi kun hanani zaman lafiya, kuma Wallahi babu ke babu dana, ko mata sun kare a duniya Yasir ba zai auri karuwa yar iska irinki ba, kuma Wallahi ke da yayarki sai mugun abun ku ya koma kanku, sai kum ga abun da ba ku so, Allah ya isa”
A nan jama’a suka shiga bata hakuri, Hajiya Fatee na fitowa daga bandaki ta dorawa Rukkaya da nata.
“Daman ban da iskanci da tsaurin ido, ke har kin isa ki taso tsugudi dake wai kin zo gaisuwa, wato ke yar iska yar daukar rahoto, to sai kije ki fada musu yadda kika tararda mu, mutuwa dai ta san gidan kowa”
Wata yayar Hajiya Kaltume ta shiga yi musu fada tana tsawarta a matsayinta na babbar duk kuwa da bata san me yake faruwa ba amman zata iya auna wasu abubuwan a kalaman da Hajiya Kaltume ta fada cewar ko mata sun kare ba zai auri Rukayya ba, a lokacin ne suka gane cewar ita din kanwar Iyami ce. A fusace Rukkaya ta mike tsaye
“Ni ma zan tabbatar miki da wani abu yau, ko maza sun yi karamci a duniya ba zan auri Yasir ba, amman gida kam idan kika ga na daina shigowa, to babu Hurriya a cikinsa”
Tana kawai ta juya, Maama da Khairy suka taso zasu yi kanta, sai da aka rike su. Hurriya ta kasa cewa komai ita dai sai mamakin yadda Hajiya Kaltume take tsanar mahaifiyarta da duk wani abu dake da alaka da mahaifiyarta take, me ye laifin Rukayya dan ta zo gaisuwa, wanda aka yi ma rasuwa da ya kamata ace ya natsu ya koma ga Allah shi ne suke haka, kamar Rukkaya ce ta yi sanadin mutuwarta. Ko da ta fito daga dakin ta sauko kasa har Rukkayya ta fice daga gidan gaba daya. A lokacin da ta fito ta duba ko’ina bata ganta ba sai ta koma bangaren Momy ta shige dakinta tana ta mamakin, ta ya Hajiya zata ce sun jidadi waye yake farinciki da mutuwar wani? Ko da kuwa nesa ne balle na kusa.
Bayan Sallah magariba Yasir ya shigo dakin nata shi ma kana ganinsa zaka san mutuwar ta taba shi, domin ya dan yi rama ga idonsa yayi ja alamar bacin rai da damuwa.
“Yayana”
Ya maida kofar dakin ya rufe.
“Hurriya, Rukkaya ta tafi?”
“Wani abu ya faru ne? Ta bar twins bata koma da su ba, kuma na kira wayarta bata daga ba sai text ta yi min yanzu wai na aiko da twins ana mata fada a gida”
“Ina suke?”
“Suna kasa, me ya faru?”
Ta yi shiru kamar ba zata fada ba gudun kar ace ta yi munafurci ko gulma.
“Hajiya ta yi mata fada, ta ce wai ta jidadin an yi mata mutuwa ai ta zo daukar rahoto ne, har tana cewa ko ita kadai ta rage ba saka aureta ba, kuma ta daina zuwa gidan nan”
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Ta furta da murya can kasa irin mai bayyana damuwa, sannan ya zauna gefeb gadon Hurriya ya dafe goshinsa.
“Ana cikin wannan halin na mutuwa me ya kawo magana irin wannan kuma? Daman sai da tace min bata son Hajiya ta yi mata wani kallo na ce ba za’ayi ba”
Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya mikawa Hurriya.
“Kira Amma idan Gwaggo ta daga ki ce mata twins za su kwana a gurinki”
“Tou”
Ta karbi wayar bayan ya cire mata password ta saka number Amma dake haddace a kanta ta kira, Gwaggo na dagawa suka gaisa ta fadawa Gwaggo kannenta za su kwana a gurinta.
“Aa ki zo ki kawo su yanzu”
“Gwaggo dan Allah, haba Gwaggo ba su tana kwana a nan ba, zan jidadi idan suka kwana za su rage min kewarku”
“Shikenan gobe amman su dawo gida, kuma ki kula da su”
“Toh Gwaggo na gode sai da safe”
Ta kashe wayar ta mika masa, ya karba ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi kofar dakin ya bude, ita ma ta sauko daga kan gadon ta bi bayansa tana jin farinciki kanenta za su kwana a tare da ita. Ko da suka sauko falon babu kowa sai Momy, yan’uwanta da suka zo gaisuwa sun tafi tun dazun. Hamid Momy na ke yi ma fada wai yana ta yi mata kiriniya a kitchen ya ki ya natsu. Yasir ko kallonsu be yi ba ya fice domin ta shi ta isheshi ga rashin yar’uwa ga damuwar abun da ya ji Hajiya Kaltume ta yi ma Rukayya, ga fadan da Rukkayya ta rubuto masa ana yi mata a gidansu, goma ta hade masa da ashirin.
“Momy ai dole su yi, saboda ba su saba ba, gidansu ko rabin kyau wannan be yi ba, kuma ba a saba ganin kayan dadi ba, sai bude fridge yake yana rufewa kamar wani tsohon bakauye”
Cewar Namra dake zaune dinning tana lasa wayarta. Maganar ta soki Hurriya irin tsokar da take jin bata zata iya mata kara ba, domin ita ma bata ti mata ba.
“Can inda suke zaune ba gidan mahaifinsu ba ne, gidan kakarsu ne, nan din dai shi ne gidan mahaifinsu”
Hurriya ya rufe na rufe baki, Momy ta matsa ta wanke mata fuska da mari.
“Dan Ubanki Namra ba yayarki ba ce kike fada mata magana any how?”
Hurriya ta dafe kuncinta ta fashe da kuka.
“Amman Momy baki ji me take fada ba? Gidan uwata take kushewa”
“Karya ta fada? Kuna da irin wannan daular a gidan uwar taku ne? Da yara sun saba da jindadi za su zo suna wannan rashin natsuwar ne? Me kuke da shi a gidan uwar taki?”
Cikin kuka Hurriya ta matsa ta rika hannun kanenta zata ja su zuwa sama sai duk suka bata fuska ganin an daki Hurriya har tana kuka, dayan ya ware hannunsa ya daga sama alamar zai daki Momy saboda ta doki Hurriya, Namra na ganin haka ta bar dinning din ta nufo inda suka ta yi masa dudu a baya.