Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Me aka yi? Waya taba ka?”
“Babu ba ayi min komai ba”
Hajiya Kaltume ta tabe baki tana murmushi.
“Kai ma dai Alhaji, a gidan nan ba zai taba Hamad ya kwana lafiya? Idan ma an fi karfinshi ai kasan yadda yake yi ma mutane ruwan duwatsu ko kuma ya shammaci mutum yayi masa wata ƙetar”
Hamad ya dago ya kalli Hajiya Kaltume da irin kallon da ya fi kama da harara, daman can shi ne mai taya Amma kishi wani lokacin, Hurriya kam team babu ruwanmu ce.
“Toh na ga yana ta bata rai ne kuma yace ba zai ci abinci ba?”
“Uhm. Hmm”
Kawai Hajiya Kaltume ta ce ta cigaba da kallon Appa dake tambayar Hamad ina yake son zama.
“Ina Hurriya zata zauna?”
“Gurin Momy”
Appa ya amsa masa.
“Nima zan zauna a can”
“Toh yayi kyau, amman dai ka saki ranka Hamad ka ji? Kuma ka ci wani abun yaushe rabonka da abinci?”
“Na sha zobo da rana”
“Zobo ai ba abinci ba ne, zaka sha tea da bread a hada maka?”
“Bana son komai Appa bana jin yunwa”
“Shikenan zan yi ma Nafisa magana sai ku maida kayanku part dinta”
Appa ya fada cikin yanayi na rashin jindadin dansa be saka komai a ciki ba. Hamad ya mike tsaye ya juya. Appa ya bishi da kallo yana fadin.
“Hamad babu ko sai da safe?”
“Sai da safe Appa”
Ya fada ba tare da juyo ba har ya fice. Hurriya ta mike tsaye domin yunwa ta matsa mata lamba.
“Appa ina tuwon?”
Appa take tambaya sai Hajiya Kaltume ta amsa mata.
“Je bangarena ki zuba ki ci, mahaifinki ya rima ci balle ku ci tare”
“Toh”
Ta nufi kofar fita da saurinta. Sai da ta fice Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.
“Dan Allah a rika kula da yaran nan, su da marayu duk daya yanzu”
“Alhaji, dan Allah na ci wannan alfarma dan Allah ko dan yaran nan, mahaifiyarsu ma tunaninsu sai ya isheta kuma kai yanzu baka lura Hamad fushi yake da kai ba?”
“Fushi me?”
“Ka kore mahaifiyarsu mana”
“Ba kin cw bata fada musu ba?”
“Eh amman ka san shi ya yafi yar’uwarsa wayo, ba mamaki ya gane, ita kanta Hurriya idan ta fahimta ba zata jidadi ba”
Appa ya sauke ajiyar zuciya.
“Ba zan iya ba ne Kaltume, gobe za a zo da motoci akwaishe mata kayanta”
“Subhanallahi Alhaji har saki nawa ka yi mata ne?”
“Daya”
“Amman za akwashe kaya da wuri haka? Wai me yayi zafi ne shi ba wuta ba? Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
Ta fashe da kuka ta mike tsaye ta fice daga dakin tana rusar kuka kamar gaske. Appa ya busar da iskar bakinsa shi kansa ya san it’s too early ace an kwashe kayan Amma a gidan daga sakinta, sai dai kiran da Bappa yake masa yake son amfani da damar ya nuna musu babu sauran zama tsakaninsada Amma, domin ya kasa amsa wayarsu tun jiya saboda be san abun da zai fada musu ba. Kai ya gigirza sannan ya tashi tsaye ya fice daga part dinsa zuwa part din Hajiya Nafisa wato Momy.
HURRIYA POV.
Hurriya na shiga bangaren Hajiya Kaltume ta samu Umm Khairi zaune a dinning tana cin nata abincin daren, da a bangaren mahaifiyarta ne sai da ta bude ta zuba amman a nan dole ta tsaya a zuba mata ko kuma a bata izinin zubawa.
“Yaya Khairi Hajiya ta ce na zuba abinci”
“Gashi nan ai dauki plate ki zuba mai isarki”
Hurriya ta dauki plate ta bude manya warmers din ta ta dauki mulmular tuwon da aka nade a leda ta raba uku ta zuba daya a plate ta rufe ta bude dayan ta zuba miyar kubewa ďanye ta saka nama da man shanu sannan ta rufe ta ja kujera har ta zauna ta tuna bata wanke hannu ba ta tashi ta shiga bandakin dake falon ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon, sai da ta yi nisa da cin abincin sannan Khairi ta kalleta.
“Hurriya”
Hurriya ta dago a hankali ta kalli yayarta Khairi wadda ta kira sunanta.
“Na’am?”
“Me Appa yace miki da ya aiko a kira ki?”
“Tambayarmu yayi ina muke son zama”
“Toh ina kika zaba?”
“Ni dai na ce gurin Gwaggo ko Hajiya, amman yace aa sai dai gurin Momy”
Khairi ta yi fuskar tausayi.
“Allah sarki, Wallahi na tausaya muku babu dadi rayuwa gidan babu uwa a gida, da ma dai Appa zai yi hakuri da ya dawo da Amma, Hurriya na ga Appa yana jin maganarki why not ki roke shi ya dawo da Amma idan ma wani laifin ta yi masa ya yafe mata”
Hurriya ta yi mata wani kallo na rashim fahimtar inda zancenta ya dosa.
“Amman zata dawo idan ta haihu ai”
“Toh Allah yasa ya maida ita, wata kila akwai gyara ai Wallahi duk ban jidadi ba dazun har da kukana”
Hurriya na jin haka sai kwakwalwarta ta dauka sarai ta gane karatun Khairi a take wani irin tashin hankali ya same ta, idonta dake cikin farin gilashi suka cika da hawaye ta kasa hade lomar tuwon dake bakinta. Slowly ta mike tsaye taja kujera baya ta fara tafiya zuciyarta na buga kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana fita falon ta watsa da gudu bangarensu da karfi ta tura kofar falon Amma ta shiga. Hamad na kwance kan kujera yana kallon remote a hannunsa.
“Hamad wai Appa sakin Amma yayi? Wai rabuwa suka yi? Yaya Khairi ta fada min”
Tana maganar yana kuka even though bata gama tabbatarwa ba. Hamad ya tashi zaune yana kallonta.
“Ai ke ce mahaukaciya shiyasa baki gane ba”
A nan Huriyya ta samu damar fashewa da kuka mai karfi, ta juya da sauri ta nufi bangaren mahaifinta.
*** *** ***
“Ah Ah Alhaji ina ce Kaltume ce Babba a gidan nan? Me zai hana su zauna a bangarenta?”
Appa ya mike tsaye.
“A nan nake son su zauna, kuma nan za su zauna ko kin yarda ko baki yarda ba, domin ke da su duk a karkashin ikona kuka kuma a gidana”
“Aa Alhaji gaskiya ban ci ƙashi ba ba zan ci aman tsoka ba! Har ina? Yara da girmansu da komai a kawo min su? Da wani abun arziki ne ai matarka take tarewa ta karbe sai a yanzu da yake wahala ce za a kawo min”
Appa ya nuna kansa.
“ƴaƴane wahala Nafisa? Ke dai har abada ba zaki taba zama matar kirki, har abada mai hali be taba fasa halinsa ba, kowa yana girma yana kara hankali da hali na gari amman ban da ke”
“Daman ni ban taba haske a idonka ba, masu haske Iyami ce da Kaltume, ka san ni ka san halina ni bana son a shiga sabgata ina bangarena babu ruwana da kowa, akan me yanzu za a dauko yayar sarauniyar gida mace da ta hana ka ganin martaba a kawo min”
Alhaji Haruna ya nuna ta da yatsansa.
“Sau daya tak bakinki ya sake furta wata magana marar dadi akan Iyami da yayanta sai mugun saba miki, ni na zabi su zauna a nan kuma a nan din za su zauna, idan baki son zama da ƴaƴana jinina ƙofar gidan a bude take..!”
Momy ta aje numfashi da karfi.
“Bismillah ga dakuna nan su zabi wanda suke so su zauna, gidan naka ne yaya naka ne ni ma taka ce Allah ya ba mu hakurin zama”
Fuuuu! Appa ya fice daga falon nata cikin mugun bacin rai. Namra da Musib suka bishi da kallo su kansu sun manta when last su ga mahaifinsu a cikin bacin rai irin wannan sai yau.
“Tsakani da Allah takurawa ce dawowarsu a nan, musamman ma dan iska yaron nan Hamad ni ubansa zan ci Wallahi”
Cewar Musib yana jin haushin hukuncin da mahaifinsu ya yanke. Bakinciki ya hana Momy sake cewa komai ta kai hannu ta dauki sarkar zinarinta dake kan aje a hannun kujera ta mike tsaye ta nufi upstairs, kamin ta isa dakinta ma wani aiki ne saboda izza da isa kamar wadda bata son taka kasa haka take tafiya.
Bakin gadonta ta zauna ta rike da sarkar sai cika take tana batsewa, ita dai ta san tana daga kafa akan kishi da matan Alhaji Haruna domin ganin take babu sa’arta a cikinsu Hajiya Kaltume dai yar talakawa ce arzikin na Alhaji Haruna Mai Yadi ne, Iyami ma haka rufin asirinsu na Alhaji Haruna ne domin har gidan da iyayenta suke ciki a yanzu shi ya siya musu shi yake dauke da nauyinsu.