VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Kullum ana fada min abubuwan da kike yi Hurriya, yaron nan ma da na rabaki da shi baki ji ba, an fada min har kyauta yake kawo miki, kuma yana zuwa kina fita hira da shi, yanzu kuma abun ya fara tsallakawa makota, to sai ki tashi ki tafi can gidan kawar ta ki ya hada ke da ita ya rike, makaranta kuma ba zan saka ki ba, ke da karatu har abada, sai dai ki ganina gurin wasu, sannan ban yarda kowa ya saka ki, sai na gani idan da karfi zaki yi karatu, babu wanda zai saka ki makaranta da yawun bakina, idan ke zaki saka kanki Bismillahi”

Hurriya ta tashi da sauri ta isa har gurin da Appa yake zaune ta rike kafarsa tana kuka.

“Appa ba ni da gata a duniyar nan sai Allah sai kai, na karbi laifina dan Allah ka yi hakuri”

“O tooo kin aikata kenan, daman na san kin yi ai, domin babu wanda zai fitar da sirrin gidan nan sai ke, kullum kina can gurin wannan Husnar ana zagina da yayana ana fadar cin amanarki matan ubanki suke, Momy ma da take rike dake bata tsira ba, balle kuma ni da kika maida abokiyar gabarki, ban da rashin hankali da tunani irin naki ta ina zaki zauna kina zagin ubanki da kawarki har mahaifinta yayi tsaurin ido ya tinkari Alhaji da wannan maganar”

Hajiya Kaltume ta fada, Hurriya ta girgiza kai da sauri, amman ta kasa magana. Kalamanta sai suka kara tunzara Appa ransa ya kara baci.

“Na fada miki, ki hada komai baki ki koma can gidansu ki zauna”

Hajiya Kaltume ta daga masa hannu.

“aa Alhaji ba za’ayi haka ba, ai sai ka kasa su kara zaginka kuma, mu ma kuma ace muna gani aka koreta, daman dai ta bata maka suna a unguwar nan, kai ne dai baka sani ba saboda sai yau Alhaji Garba ya same ka da wannan maganar, amman zance kala kala ni na ji, Nafisa ma ta ji, kawai dai muna shakkar fada maka ne saboda baka yarda da komai aka fada maka na Hurriya, duk da haka dai ba zan ce ka koreta ba domin bata gidan da ya fi wannan”

Hurriya ta kalleta tana kuka.

“Haba Hajiya ki ji tsoron Allah ki rika fadar gaskiya, bana zuwa ko’ina sai gidansu Husna ita ma ba kullum ba, Wallahi ban taba zaunawa wani guri na zagi Appana ba…”

Hajiya Kaltume ta rufe baki.

“Laa ke ni da nake miki yaki saboda kar ya koreki, shi ne zaki dubi idona ki ce na ji tsoron Allah na fadi gaskiya, to da can tsoronki nake ji ne? Alhaji ka ji min wata magana?”

Appa ya mike tsaye yana kokarin fisge kafarsa, domin ransa a matukar bace yake, Hurriya kuma ta kara rike kafar har sai da ya dago fuskarta ya dauketa da mari.

“Ba zaki sake min kafa ba, ki tafi can gurin wanda kika dauka ubanki ki zauna a gidansa, kuma daga yau sai yau ban yafe miki ba idan kika sake furta wata kalma marar dadi akan Hajiya”

“Ba zan saka bakina ba, kar ki rufe ni da duka”

Hurriya ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya ta kwanta a gurin tana ta bawa Appa hakuri amman be saurare ba ya yayi ficewarsa.

“Toh sai ki tashi ki koma gidansu kawar taki da kuke munafurcin tare, daman Allah kadai ya san zagin da kuka min, uwarta ma ai yar gidan Iyami ce kin ga zata fi jindadin rike ki”

Hurriya ta dago ta hade hannayenta.

“Dan Allah ki yi hakuri, ki bawa Appa hakuri Wallahi ban kai kararku ko’ina ba, kuma ban zauna na zageku da kowa ba”

“Yanzu dai ki tashi ga kofa can ki fice min daga daki, kuma idan ba kina son fushin Appanki ya karu ba ne zai fi miki kyau ki bar gidan, idan ma gurin kawar zaki koma sai ki koma, idan kuma kina son kara janyowa kanki wata matsalar ne ga fili ga doki”

Ta karasa tana nuna mata kofa. Hurriya ta mike tsaye ta fice daga dakin tana kuka sosai, downstairs ta sauko ta a nan ta hadu da Khairy dake zaune ta hade rai.

“Yaya Khairy dan Allah ki bawa Appa hakuri, dan Allah Wallahi ban kai kararsa ko’ina ba”

Khairy ta fisge hannunta.

“Wannan ya zama karon na karshe da Fadeel zai ce ki dauko masa wani ki dauko, banza mai zubin karuwai ko wane namiji sai kin san yadda kika yi kika ja hankalinsa gareki”

Ta tashi daga gurin ta nufi hanyar stairs, Hurriya ta bita da kallo hawaye dake mata zuba suna kokarin katsewa, ita kuma yanzu kishi take da ita ko minene? Beside ita da uwarta su suka shirya mata duk wani kulle kulle a gidan. Juyawa ta yi ta fuskanci kofa ta fara takawa har ta fice, bangarensu Namra ta nufa, ko da ta shiga falon babu hawaye a idonta dan haka babu mai sanin ta yi kuka sai idan an kalli idonta da kyau. Ba tare da ta tsaya kula da kowa na falon ba ta nufi stairs sai Momy ta kirata.

“Hurriya”

Ta juyo sai dai bata daga kai ta kalleta ba.

“Me yasa kika kai karar bakinga gurin mahaifinsu Husna?”

“Ko da na fada be zama lallai ku yarda ba, amman ni ban kai karar Appa ba, ban san dalilin mahaifinta na samun Appa da maganar karatuna ba”

“Allah kyauta, iya baki dai yana da kyau muma Allah kadai ya san irin zagin da zaki jan mana”

Hurriya ta juya ta ta cigaba da tafiyarta, sai da ta isa bakin kofar dakinta sannan hawaye suka zubo mata. Ta murda kofar ta bude ta shiga, sai ta samu kanta tsaye tana fuskantar madubin dake gabanta, wata macen mai kama da ita take gani, mai tsananin rauni da damuwa, cikin zuciyarta take hangowa mai cike da kunci da bakinciki. Takawa ta yi kamar mai koyon tatata ta isa gaban madubin dake dakin tana kallon Innocent face dinta.

“Rarrashi nake so, babu mai yi min, gata nake nema na rasa shi ta ko’ina, rayuwa a gidan da babu uwa akwai wahala ko da tana raye, farinciki neman gagarata yake yi, me na tare musu ne? Wane laifi na aikata wa kowa yake ta tsanata? Dan wannan abun har ya kai Appa ya koreni? Kuma babu wanda zai bashi hakuri?”

Magana take da kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta dake zube a jikin madubin.

‘Ba komai yake bukatar kuka ba Hurriya, wani abun jajircewa yake bukata, ki karfafawa kanki guiwa, ki goyi bayan kanki, sannan kuma ki saurari zuciyarki, idan babu mai kaunarki ki kaunaci kanki, nuna musu zaki iya karki yi kasa a guiwa, wata rana ke uwa ce, irin wannan matsalolin ke zaki magancewa yayanki…’

Wani ne ya kamata ace ya tsaya a gafenta ya fada mata wannan, akasin haka zuciyarta ce ke karanta mata karantun da a yanzu ta shirya daukarsa, domin a yanzu ne idonta ya bude zuciyarta kuma take kokarin waraka da rauni. Hannu ta saka ta share hawayenta na dama zuwa hagu, sannan ta yi murmushi ta juya cikin kuzari ta fara hada kayanta. Abubuwan da ta san zata fi bukata ta hada a luggage ta ta dauki Qur’anenta ta fito daga dakin, ta fara saukowa a hankali sai da ta sauko falo sannan ta kalli Momy ta ce.

“Momy zan tafi?”

“Ina?”

Momy ta duba ta da mamaki.

“Ina?”

“Appa ya ce na bar masa gidansa”

“Saboda wannan abun?”

Hurriya ta yi shiru bata ce komai ba. Momy ta tashi tsaye.

“Ina zuwa, ki bar gidan ki tafi ina?”

Ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Appa, kamin ta karasa Hurriya ta ce.

“Momy ko kin tafi ba zai hakura ba, ransa ya bace sosai”

Momy ta juyo.

“Daman na san za a rina, yadda Kaltume ta kori uwarki wata rana sai ta koreki a gidan nan, ke ma kuma baki jin magana tun da kin san halin mahaifinki a yanzu ai ya kamata ki kiyaye, miye na zuwa ki yi tseguminsa da kawarki har magana ta dawo kunnensa”

Hurriya ta sauke kanta kasa, ita kanta bata san yadda zata warware wannan abun ba, balle kuma su da suke kallonta a munafuka. Namra ta sauko rike da leda ta mikawa Hurriya dake tsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected