Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ta karasa cikin kuka.
“Dole ayi masa jefa mana, a kauye ne wane Malami ne yake irin aikinsa? Babu shi kuma gashi Allah ya amince masa komai girman gona ko gida sai aji Malam be ya siye va dole hankalinsu ya tashi ba, mota ma wannan wanda Malam yake hawa abar kallo ce”
Hajiya Kaltume ta Kalli babbar matarsa tace.
“Amman duk wanda ya aikata nasa wannan abun mu ya aikatawa ba Malam ba, mu ya jefa a matsala”
“Haka kowa yake fada, ga Malam da mutane manyan mutane kala kala gari gari zuwa ake saboda iya aikinsa, kowa ya zo cewa yake ba mu aka yi ma mutuwa ba su aka yi ma”
“Wannan abu be yi dadi ba, Kawata na kiran wayarsa a kashe kullum ina sauraren ko zai kira amman shiru ashe wani labarin ake na dabam”
“Malam ai be fita da komai ba, wayarsa ko ganinta ba ayi ba”
Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya, idanuwanta suntun suntu tsabar kukan da tasha.
“Kuma be bar muku sakon komai ba?”
“Ina zancen barin sako a mutuwar da ba a san da zuwanta ba balle a shirya mata, kuma ko da ya bar wani abu ai wuta ta kone komai ina za a gani ma”
“Ba shi nake nufi ba, sako haka ko na kalami cewar an turo masa kudi ko kuma kudin da filin da yake guri kaza ba nasw ba ne? Ko gona?”
“Aa babu kayan kowa a hannun Malam, domin idan ya siye gida ko gona ko fili ya kan kiramu ya fada mana cewar gidan da yake guri kaza ko fili ko gona sun zama mallakinsa ya siye, har takardun da ake yi na shaida yana nuna mana, kuma yawanci idan sai siya da aminsa yake zuwa Malam Musa, bayan rasuwarsa kuma Malam Musa ya hannata mana komai na Malam kuma ya bi mutane da dan abun da yake hannun malam na mutane aka biya, babu hakkin kowa a gurin Malam yanzu”
“Da dai zan samu ganin Malam Musa na yi magana da shi, saboda akwai mai yawa da na turo masa a account da sunan zai tafi gurin Malaminsa yayi min aiki, kuma kawata ma Hajiya Fatee ta bashi kudi mai yawa ya siya nata gona da fili a kauye, da zan ga Malam Musa sai na tambaye shi ko ya san wani abu a kai”
“Gaskiya babu, kuma wani be taba zuwa mana da irin wannan maganar ba sai ke, amman saboda kaucewa zargi, bari a kira Malam Musa sai ku yi magana da shi”
Amaryar ce ta aika yaro gurin da ta san aminin mijinta na zama aka kirashi, da ya iso ya shigo cikin gidan suka gaisa da Hajiya Kaltume ta yi masa gaisuwa sannan ta kora da bayani.
“Ni sunana Hajiya Kaltume akwai kawata Hajiya Fatee tana mota yanzu haka, mutuwar ta taba ta sosai ba zata iya takowa nan ba, ni na tura masa kudi kwana goma da suka wuce ko sha daya, kudi mai yawa akan cewar zai kawai Malaminsa ayi min aiki domin wannan aikin ya fi karfinsa, yace Malaminsa zai siye rakumi da kayan aiki, shi ne nake tambayar ko ka san wani abu akan haka”
Mutumen da ake kira da Malam Musa ya girgiza kai.
“Aa Wallahi be yi wata magana kamanciyar wannan ba, kuma Malam ai Malaminsa ya dade da rasuwa shekara kusan goma sha wani abu yanzu”
Hajiya Kaltume ta yi tagume.
“Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un…”
Tana jin wani sabon kuka na taso mata.
“Ita kawata dake mota har filaye take bashi kudi ya siya mata da gona ita be yi maganarta ba ko? Ko kuma ya bar wata wasiya? Ko a cikin gidajen da yake siye yace wannan na Hajiya Fatee ne ko na wata”
“Aa babu wannan, Malam be taba fada min haka ba, Maimuna a cikinku akwai wanda ta taba jin magana makamanciyar wannan abakin Malam”
Uwar gidan ta girgiza kai.
“Aa ai na fada mata ba mu san wani abu da Malam ya siye ya ce na wani ne ba, sai dai idan sheri za’ayi masa anji ya bar dukiya a haka kai da mutanen birni azo ace za a kwace”
“Aiko ba zata sabu ba, komai ai sai da hujja ake yinsa, Malam yana kafa shaida idan zai siye abu, har takardu ana yi sai dai wutar da ta kone komai yasa ba a tsira da takardun ba, amman shaidu ai suna nan da ransu, babu wanda ya isa ya zo mana daga wani guri da sunan dan boko ya karbi duniyar Malam, idan ma manufar ku kenan to tun wuri ku tashi ku kama hanyar garinku ko na tara muku mutane yanzu nan”
Hajiya Kaltume ta daga kai ta kali mutumen da ya mike tsaye yana nuna mata kofar fita bakinsa da asuwaki hannunsa kuma rike da carbi.
“Indai kai aminin Malam ne tabbas ka san gaskiya sai idan cinye dukiyar zaku yi, zan tafi amman ba zamu kyale wannan maganar ba”
Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fice a gidan cikin bacin rai tsabanin shigowar da ta yi da zullumi. A mota ta tararda Hajiya Fatee ta fito da kafafuwanta waje tana zaune daga ciki ta jingina da motar.
“Malam ya mutu, kuma ta tafi da dukiyarmu amman na ke kin yi wauta Hajiya Fatee kuma kin yi sakarci irin haka ake gudu daman, Malam be bar wata wasiya akan kudinki ko gonakin da yake cewa ya siya miki ba, kuma babu wata shaida ke ma kuma baki nemi ya baki shaidar komai ba lokacin da yake raye, yanzu ga irin ta nan nan ke baki ga duniyarki ni kuma ba ni ga aiki ba kudin rakumi….!”
“Ni ai idai wannan abun ba zai tashi ba, kudin mai sauki ne indai wannan abin kunyar ba zai bayyanar min ba to zan iya hakura da komai”
Direban ya kai dubansa garesu.
“Subhanallahi wai Malamin da kuka zo gurinsa ne ya rasu?”
“Ba a sani ba, ina ruwanka? Ka kama bakinka ka yi abun da ya kawo ka, ba gulma da sa’ido ba”
“Ah Hajiya daga tambaya Allah ya baku hakuri, ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni”
Ya bude da yake jingine ya shiga ya rufe.
“Shiga mota mu tafi Hajiya Kaltume, zancen gida da gona zamu yi tunanin abun da ya kamata mu yi daga baya”
Hajiya Kaltume ta juya ta dayan bangaren ta shiga motar, tana kuka.
“Abubuwa duk sun lalace min, idan na taba nan wani gurin ne zai kwance, idan na dawo ta nan wani gurin kuma sai ya balle, ina saka ran za’ayi min aiki na samu sauki wannan rayuwa da nake ciki sai kuma mu zo mu tararda bakin labari wannan abu da me yayi kama… ”
“Ke naki ai duk mai sauki ne, ni cw a ruwa tsundun kuma babu tudun dafawa”
Haka suka yi ta juya zancen suna bakinciki da kukan da ya mantar da su akwau bandits a hanya, direban yana sauke su a gidan Hajiya Fatee yayi tafiyarsa. A bakin kofar dakin Hajiya Kaltume ta zube zaune ta cire mayafi ta je jaka a gefe tana kuka.
NAMRA POV.
Gaba daya ta jika screen din wayarta da hawayen dake zuba a idonta, hoton Captain take kallona gurin da yake sanye da kayan sojoji yana daga tsaye aka dauke shi hoto. Ta san ta yi rashi na har bada domin abu ne mai wahala a yanzu Captain yace zai dawo ya aureta ko da kuwa ya rabu da Hurriya, ta san ba haramun ba ne amman ai da kunya, ace miji ya saki kanwa ya auri yaya, kuma yadda ta san halin dan’uwanta ba zai aminta ya aikata haka ba.
“Tun farkon zuwanki bangaren nan, ban miki komai ba sai alheri, ke kika saka na canja ashe ma kara da na canja domin kin nuna min cewar ke ba halak ba ce mai tausayi, kin raba ni da Salim na hakura ina murna Allah zai musanya min da ďan’uwan sai kuma ki zo ki karbe min shi? Baki ji kunya ba? Kin raba yayarki da samari har biyu?”
Ta runtse ido tana kuka.
“Ina sonka Captain ina sonka me yasa baka gane ba, duk zuwan da kake gidan nan baka fahimci hakan ba? Ko kuma dai Hurriya ta dauke maka hankali ne saboda ta fi ni kyau? Me ya rude ka ka auri yarinyar da ba ajinka ba, yarinyar da bata dace da kai ba, irin wannan jihadin da ka yi a finafinai nake ganin yana faruwa, ko kuma a wasu kasashen turawa amman ba gidab Malam Bahaushe ba, waya ce maka hakan zai baka kwanciyar hankali? Me yasa zuciyarka bata shawarce karka aikata ba?”