VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Appa yayi murmushi a yayin da yake zaune a kasa rike da sarka ya kalli Yasir dake gefensa ya mika masa sarka.

“Budewa Hajiya ta gani”

Yasir ya karba ya mike tsaye ya bude mata sarka, Hajiya Binta ta saka hannu ta karba idonta na cika da hawaye.

“Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar, Allah ka sakawa wannan auren Albarka, kuma ka nuna min na sauran yaran”

“Amin Hajiya Amin”

Appa ya amsa da kansa, fadar irin farinciki da yake ciki a yanzu bata lokaci ne, farinciki da yake a yanzu ya fi wanda ya samu kansa a lokacin da aka haifo masa ita.

“Be kamata mu zauna ba Tsoho tafiya zamu yi mu sanar gidan mahaifiyarta da kuma ita yarinyar halin da ake ciki”

“Haka ne… ”

A nan kam sai yanayin Appa ya canja, ya sauke kai kasa damuwa na bayyana a fuskarsa. Yasir ya aje sarkar zinarin dake hannunsa ya mike tsaye ya fice daga dakin yana taba wayarsa. Appa ya bishi da kallo har ya fice sannan ya juyo da kansa ta inda Hajiya Binta take zaune ya ce.

“Ina jin kunyar hada ido da mahaifiyar yarinyar Hajiya, abun da na yi mata ban kyau ba, be kamata na aikata hakan ba, ban san me yasa na sake ta ba, kuma na kasa samun dalilin har yanzu da muke maganar nan dake, Iyami bata min komai ba face biyayya da kyautatawa, amman na saka mata da mafi munin sakamako na juya mata baya na wulakanta yaran da ta haifa min”

Ya shigar da lips dinsa duka biyu a bakinsa ya rufe dantse bakin zuciyarsa na ƙuna da abun da bakinsa yake furtawa.

“Alhamdulillah, ganin ka gane kuskure ni a gurina abun farinciki ne, babu daren da bana addu’ar Allah ya baka ikon gane gaskiya, domin abun da ka aikata kamar baka aikata shi cikin hayyacinka ba”

“Ban san me ya rufe min ido na aikata haka ba, ina jin nauyin iyayenta da ita kanta Iyamin a yanzu”

“Ka kawar da komai a ranka, daman shi aure ya gaji haka, a tsaba kuma a shirya ko a yanzu dare be maka ba, lokaci be kure ba zaka iya gyara inda ka yi kuskure ka share inda ka bata, kar wannan jin nauyin ya hanaka sanar da yarka Hurriya cewar ka bada aurenta a yau, kai da kanka nake son ka fada mata wannan”

Ya amsa mata da kai sannan ya mike tsaye yana hade rigarsa.

“Zamu jiraki a waje Hajiya sai ki shirya mu tafi”

“Toh…”

A waje suka jira Hajiya ta fito tana rike da sadakin jikarta, ta shiga baya Appa da Yasir kuma suka shiga gaba. A motar Hajiya sai godiya take yi ma Allah na yadda ya kawo auren Hurriya a kusa kuma da mutumen da ba ayi tsammani ba, Appa kuma fargaba da kunya na lullube shi a yayin da Yasir yake kara kusanta gidansu Gwaggo.

“Ni na manta ban tambaya ba, yaron dai yana da kirki ko? Murna da farinciki sun mantar da ni wannan”

“Ba shi matsala Hajiya na san shi, yana da kirki kuma babu wanda zai fadi sherinsa, Hurriya ta yi dacen miji fatan mu dai Allah ya bata lafiya kuma ya basu zaman lafiya”

Hajiya Binta farinciki sai ya kara ninkuwa, ta kara yi ma Allah godiya.

 

HURRIYA POV.

“Wannan jaraba da kuke ta fadawa Allah ya yaye muku, idan wannan ya wuce sai kuma wani ya zo, ke kin tashi baki ya bude ita kuma ido ya rufe”

Gwaggo ta kalli Hindu wanda ke kallon Hurriya tana lalaben gini har ta iso gurin da Amma take zaune tare da Gwaggo da kawar Amma wato Hindu ta zauna.

“Abun da Allah yayi annabi sai ceto, likitocin sun ce wai damuwarce ta taba mata ido, amman ni ban yarda ba na fi zaton wani aikin ne aka yi mata idon ya rufe gaba daya, gashi an yada hotunanta kin ga shikenan an gama da rayuwarta, ba ido balle ta yi karatu ta gina kanta kuma babu wanda zai aureta a haka”

Hindu ta rafka uban tagumi.

“Oh Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un, wannan mugun kishi da me yayi kama? To ko ita ma za mu nema mata taimakon a gurin da aka nemawa Amma? Tun da gashi dai mun fara ganin haske”

Amma ta kama Hurriya ta kwantar da ita a cinyarta hawaye na sauko mata.

“Mun dai ga haske Hindu, Wallahi ban dauka zan iya kara yin magana ba, na dauka kalmaina sun kare a duniyar nan, ina kallon abu na zan iya cewa a bani ba, ina da maganganu da yawa a bakina amman ba zan iya furta ko daya ba, bana iya motsa jiki bana iya komai, amman ki duba yanzu magana fa nake yi, bana jin karfi a jikina sosai amman Alhamdulillah na gode Allah”

“Shi ma duk zai bari da yardar Allah, lafiya daman da rarafe take shiga a jiki har a tashi tsaye, ciwo ne yake jefar da mutum farat daya”

Cewar Hindu. Kamin su daga kansu gaba daya su kalli kofar gidan, Hajiya Binta ce ta shigo Appa yana bayanta sai Yasir a bayan Appa.

“Sallamu Alaikum”

Gwaggo da Hindu suka amsa mata, Amma kuma ta sauke kai kasa tana nadamar kallon Appa da ta yi kamar wanda ta yi arba da bakin maciji.

“Maa Shaa Allahu, Iyami ce a waje? Haka nake so lafiya ta samu”

“Alhamdulillah, Rukkaya dauko tabarma ki kawo ma baki”

Gwaggo ta amsa tana bawa Rukkaya umarni. Appa ya kasa daga ido ya kalli kowa kamar wanda ya aikata abun kunya. Rukkaya ta fito rike da tabarmar ta shimfida kusa da wanda Amma take zaune. Hajiya ta fara zaunawa sannan Appa Yasir, daman haka tarbiyar take, sai iyayen sun fara zama ake zama, idan kuma suna zaune ba ka tsaya a kansu ba sai dai rankwafa ko na zauna a kasa.

“Jama’a ina kwananku ko wuni zan ce domin dai yanzu ai 12pm ta yi”

“Lafiya Kalau Hajiya ya gidan”

Gwaggo ta amsa ba yabo ba fallasa. Appa ma ya mikawa Gwaggo gaisuwa, ba dan yana a gaban Hajiya Binta ba da kuma tunanin dalilin zuwansa wata kila da ba zata amsa gaisuwar Appa ba.

“Lafiya Kalau”

Amma ta daga kai ta kalli Rukayya dake zaune ta ce.

“Dauko min hijabina Rukayya”

A rude Appa ya dago kai ya kalli Amma, Hajiya Binta ma ta kalleta Yasir ma kallonta, dukansu sun yi turus suna mamakin jin furuci ya fito daga bakinta.

“Iyami kina iya magana yanzu?”

“Allah ya nufa Hajiya”

Amma ta guntun murmushi tana amsawa Hajiya Binta dake rike da baki.

“Allah da iko kake, kai Alhamdulillah yau farinciki ya mana yawa”

“Amma….”

Yasir ya kirata sai ta kalleshi ta yi murmushi ta amsa.

“Na’am Yasir”

“Alhamdulillahi”

Wannan karon Appa ne ya jaddada godiyarsa ga Allah yana kallon Amma, irin kallon da ya dauki shekaru be yi mata ba, nadama da damuwa bayyane a fuskarsa karara. Rukkayya ta kawo Hijab ta mikawa Amma, sai Amman ta karba ta saka domin tana ganin Appa da Yasir ba muharramanta ba ne a yanzu.

“Hurriya ta so mahaifinki na son magana da ke”

Hurriya ta amsa kiran da Hajiya Binta ta yi mata ta tashi zaune, sai ta lalaba ta matsa gurin da Hajiya take ta zauna, Appa ya kai hannayensa ya kama nata hannayen ya juyo da ita ta fuskance sai ta nade kafafuwanta irin zaman da musulunci ya koya mana yayin da zamu ci abinci, wato ta nade kafafuwanta tana fuskantar mahaifinta.
A lokacin da Appa ya kalli yarsa sai tausayinta da kaunarta da kuma kunyarta a lokaci daya mamayeshi. Ya sauke ajiyar zuciya sau uku sai a hudu ya samu damar hada kalmomin da zai gamsar da yarsa da su ya hada guri daya ya fara magana.

“Hurriya na san kin san cewar ni mahaifinki ne, a cikin abubuwan da Allah ya dora min nauyinsu akwai ciyar da ke da shayar da ke da tufatar da ke da halak, idan kuma kin kai munzali Annabi yace na zaba miki mijin na kwarai wanda na yarda da addinsa da dabi’arsa kuma mai abun yi. Ban sani ba ko na kokarta a tarbiyarki, wata kila na yi jarumta a ciyar da ke da tufatarwa, ba zan gane hakan ba sai ranar alkiyama, a cikin kokarin sauke nauyin da Allah ya dora min, na aiwatar da wani a yau. Yake ƴata yau kina zaune a gabana ne a matsayin matar wani, wanda cin ki da sha da tufatarwarki za su koma a kansa, a yau kin shiga sahun manyan mata, a yau kin tashi daga budurwar kin zama matar aure, daga yau ladarki zata riɓanyya har zuwa lokacin da za ki bar duniya, neman aljannarki a yau ya sauka daga kan kafata ya koma karkashin kafar mijinki…. A yau na aurar da ke Hurriya…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected